Mayu 15, 2017 08:17 UTC

Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na Yau zai bayyana kan dabi'ar rigeggeniya wajen aiki alheri .amma kafin shiga cikin Shirin sai a dakace mu da wannan.

*************************Musuc*******************************

Masu saurare, dabi'ar aikata alheri na daga cikin kyawawen dabi'un musulinci da Ma'aikin Allah (s.a.w.a) gami da shugabanin Shiriya na iyalan gidan Anbata tsarkaka suka yi wasici kansa, a cikin Littafin Awa'il Li'aly(عوالي اللئالي), an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka yace:( Duk wanda kofar alheri ta bude masa to ya gaggauta aikata shi domin bai san lokacin da za a rufe masa ba), Masu saurare hakika daga cikin tabbacin dabi'antuwa da wannan dabi'a mai albarka, Mutum ya yi amfani da kwanukan rayuwarsa wajen aikata aiyukan alheri,Shekh Saduk cikin Littafinsa na Man La Yahduruhul-Fakih ya rauwaito Haidisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(Babu wata rana da za ta zo da Dan Adam sai ta fada masa cewa Ni sabuwar Rana ce kuma Ni a gareka Shaida ce, ka fadi alheri a ciki Na wato a cikin wannan Rana kuma ka aikata alheri da zan yi maka sheda ranar Alkiyama, Hakika bayan yau din ba zaka sake ganni ba har abada), kuma a wajen kodayinsa na gyaran Mumunai, Imam (a.s) ya kasance ya na jadadda wasiyar sa a gare su na su dabi'antu da dabi'ar amfani da Lokaci wajen aikata alheri tun kafin ya gushe, Hakika babban malamin nan Nu'uman Magribi ya nakalto Hadisi daga Shugabanin Shiriya Imam Sajjad da Imam Bakir (a.s) sun nakalto wasiyar da Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib  (a.s) ya yi kafin mutuwarsa inda yake cewa:(Na yi muku wasici da aiki kafin lokacin da kuke da shi  ya gushe, ku yi amfani da lafiyarku kafin rashin lafiya ta same ku, kuma kafin Rai ta ce (Kaicona  game da abin da na yi sakaci na hakkin Allah, Hakika ni na kasance daga masu yin izgili* ko kuma ya ce"Da Allah ya shirye ne da lallai na kasance daga masu tsoron (azabarsa)). Masu Saurare hakika hadisin da ya gabata ya tabbatar mana da cewa dabi'antuwa da dabi'ar gaggauta aikata alheri na cikin wasiyoyin Allah madaukakin sarki a cikin Alkur'anin sa mai girma, kuma an  yin istinbati a cikin Ayoyi da dama na Alkur'ani mai tsarki da suke bayyani kan halin masu fice iyaka ta yadda ba su yi amfani da Lokacin su ba wajen aikata alheri a Duniya kuma suna kiran kaico da hasarar su a ranar Alkiyama, domin haka ne aka sanya wa daya daga cikin Surar Alkur'ani mai tsarki Suratu Tagabun wato ranar Kamunga, A cikin Littafin Iddatu Da'I,( (عدة الداعي an ruwaito Hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, dangane da dalilin da ya sanya aka kira wannan Surat da Suratu Tagabun cewa ranar Alkiyama za a budewa Mutum taskar aiyukansa da ta hada da dukkanin kwanuka, ayoyinsa na Duniya  za ya ga ba komai ciki domin bai aikata komai a cikin sa ba, Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(bayan anbaton wannan Aya, sai ya ce domin a wannan rana za a gwada ma Bawa taskar lokacin da yayi a Duniya inda cikin kaico da nadamar da ba ta da amfani, saboda bai aikata komai na alheri a cikin sa ba, alhali kuma yana iya cika sa da aiyukan da ba za a iya misalta su ba).

**************************Musuc*****************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa kuma kadda a sha'afa shirin na zababbun aiyuka na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, Hakika masu saurare musabaka wajen aikata alheri na daga cikin mafi martaba na dabi'un masoyan Allah da Nassosi da dama suka yi kira kansu, Na'am hakika Allah madaukakin sarki ya yabawa  wadanda suka dabi'antu da wannan dabi'a a cikin Littafin mai tsarki, inda ya ce: (Wadannan su ne suke gaggawa ga aikata alhairai,suna kuma masu rige-rige gare su) suratu Muminuna Aya ta 61, haka zalika Annabawan Allah amincin Allah ya tabbata a gare su sun yabi masu wannan dabi'a mai girma, a cikin Suratu Anbiya'I bayan an Ambato wani gungu daga cikin su da kuma na karshen su Annabi Zakariya sai Allah madaukakin sarki ya ce:(Sai Muka amsa masa Muka kuma bashi yahaya, Muka kuma gyara masa (mahaifar) matarsa.Hakika su (wadannan annabawan) sun kasance suna gaggawa wajen yin alhairai suna kuma rokon Mu suna masu kwadayin(rahamarmu) kuma masu tsoron (azabarmu), sun kuma zamo masu kaskantar da kai gare Mu) suratu Anbiya'I Aya ta 90.masu saurare daga cikin misdakin dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a ta Annabawa shi ne rige-rige wajen amfani da lokaci a aiyukan alheri. Hakika a bangaren Shi'a da Sunna an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(ku gaggauta aiyuka na gari kafin ku shagaltu) a cikin Littafin Awalil Li'aly(عوالي اللئالئ) an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) na cewa:(barin Dama, bakin ciki ne da kuma tsananin damuwa, Dama tana ficewa kamar yadda girgije  ke ficewa).domin haka masu saurare hadisai sun bayyana karahiyar gaggauwa a kan al'amura face a kan aikin alheri, A cikin Littafin Kafi na Sikatu Islam Kulaini an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Hakika Allah ya na son Aikin alheri da aka gaggauta aikata shi), A cikin Littafin Guraru Hikam an ruwaito hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) kuma wasiyin Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:( Nazari a kan komai abin yabo ne face a kan damar da ta zo na aikin alheri) har ila yau cikin wani hadisi na daban Imam (a.s)ya ce :(Nutsuwa  ya fi alheri a kan gaggawa face wajen damar biyayya da aikata alheri, Dama tana ficewa da sauri, kuma ta nada yuwar komowa, Dama tana ficewa kamar yadda girgije ke ficewa, ku riki damar ku a kofofin alheri, idan kuma ba haka ba za ku dawo cikin Nadama). Masu saurare, dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a na daga cikin sanadiyar samun rabauta a Duniya da Lahira, kamar yadda Shugaban Muminai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya shiryar da mu a riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Guraru Hikam, Imam (a.s) ya ce:(mafi rabo daga cikin Mutane shi ne wanda ya gaggauta aikata alheri, kuma ya ji dadi a wajen riga-rigen aikata aiyukan alheri da kuma tsarkakakun aiyuka) da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu damar aikata wannan kyakkyawar dabi'a domin albarkar riko da wasicin Annabin Rahama (s.a.w.a) da kuma na iyalan gidansa tsarkaka.

**********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.

 

 

Ra'ayi