Mar 07, 2016 14:06 UTC

Yau Asabar 22 –Esfan-1394 H.Sh=02-Jamada-Thani -1437H.K.=12-Maris-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 85 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-maris-1930M. Mutanen kasar India karkashin jagorancin Mahatma Ghandi sun fara wani yunkuri na nuna rashin amincewa da Karin kudin fito na gishiri wanda turawan Ingila yan mulkin mallaka suka yi. Ghandi tare da magoya bayansa kimanii dubu 78 sun je bakin teku inda suka samar da gishiri mai yawa wanda zai isa mutane da dama a kasar. Turawan sun tura jami’an tsaronsu wadanda suka kama dubban magoyan bayan Ghandi suka tsare, sai dai yunkurin mutanen daga karshe ya kai ga nasara inda turawan suka janye dokar ta Karin kudin fiton gishiri.


02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 47 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Maris-1968M. Tsibirin Moris daga yankin Kudancin Africa ta sami ‘yencin kai daga turawan Ingila yan mulkin mallaka. Turawan Holand ne suka fara yiwa tsibirin Moris muslkin Mallaka a cikin karshe na 17 miladia. Sai kuma a shekara 1814 miladiya turawan Ingila suka maye gurbinsu a mamayar tsibirin na Moris. Wannan halin ya ci gaba har zuwa lokacinda mutanen kasar suka fara fafatwa don samun ‘yencin kai, sannan majalisar dinkin duniya ta shawarci turawan su mikawa mutanen Moris ‘yencin kansu, a nan ne a shekara ta 1968M turawan suka yada kollon magoro suka huta da kuda inda suka mikawa mutanen tsibirin Moris ‘yencin kai. Kasar Moris dai tana da fadin kasa kilomita murabba’ee 2000 sannan tana da mutane yan asalin kasar kimani miliyon guda.


03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 35 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Esfand-1358H.SH. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jumhuriyar musulunci ta Iran ya bada umurnin kafa cibiya ta kula da iyalan shahidan juyin juya halin musulunci. A wani bayani da ya gabatar, Imam ya bayyana cewa “ kowa daga cikimmu ya san irin sadaukar da kai wanda shahidan juyin juya halin musulunci suka yi a kan wannan tafarki ta neman yerdar All.. amma duk gudun mawan da wani ya bayar bai kai na shahidai da wadanda suka sami tawaya a cikin rayuwarsu ba. Don haka ya zama wajibi a samar da cibiya ta musamman don kula da iyalan wadan nan masu sadaukarwa. Da haka kuma aka samar da “Mu’assar Shidai “ a nan Iran wacce take daukar nauyin iyalan shahidai na juyin juya hali da kuma nay akin Iraqi har’ila yau da iyalan duk wadanda wata cuta ta samesu kan wannan tafarkin.

Tags

Ra'ayi