Mar 09, 2016 18:02 UTC

Yau Alhamis 27 – Esfand-1394 H.SH=07-Jamada-Thani-1437H.K.=17-Maris-2016M.


01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 68 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Maris- 1947M. Kasashen turai guda hudu wato Britania, Faransa, Beljika da kuma Holand sun kulla wata yerjejenia ta taimakawa juna a fagen tsaro da kuma tattalin arziki a birnin Brussels na kasar Beljika. Yerjejeniyar wacce ta fi shahara da “Yerjejeniyar Brussels” it ace ta zama harsashin kafa kungiyar tsaro na NATO daga baya.  Sannan bayan yan watanni kasashen suka gudanar da wani taro a birnin Washinton na kasar Amurka tare da gwamnatocin Amurka da Canada da kuma wasu kasashen yammacin Turai  inda a nan ne , a ranar 1-Afrilu-1949M aka kafa kungiyar tsaro ta NATO.


02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 20 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Esfanda-1374H.SH. Aya. Abul-kasim Rahamani Khalil wani babban malami a nan kasar Iran ya rasu. An haifi Aya. Khalil a shekara ta 1302 H.SH a garin Beh-shahar a arewacin kasar Iran. Ya fara karatu a gida sannan yana dan shekara 23 ya je birnin Najaf na kasar Iraqi inda ya kamala karatu a gaban manya manyan malamai a birnin. Sai kuma a shekara ta 1338 H.SH. ya dawo gida ya fara karantarwa na tsawon shekaru 10 a nan birnin Tehran. Sai kuma bayan hake ya koma birnin Qum da zama da kuma ci gaba da wallafe wallafe. Daga cikin littafann da Aya. Rahmani Khalil ya wallafa akwai  «تفسیر سوره حمد»، «رساله در طلب و اراده» و «نامه ها و مکتوبات عرفانی».


03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa 14 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Esfanda-1380H.SH. Aya. Mohammad Muzaffari Qazwini ya rasu a nan Iran.  An haifi Aya. Qazwini a shekara ta 1304 a garin Qazwin dake yammacin birnin Tehran. Ya kuma fara karatun sharara fage a gida. Daga nan ya ji birnin Qum inda ya ci gaba da karatu. Daga kaeshe ya kamala karatu a gaban manya manyan malamai na zamaninsa a birnin Najaf na kasar Iraqi. Sai kuma a shekara 1352 H.SH ya dawo garinsu Qazvin inda ya ci gaba da karatu da kuma karantarwa. Aya. Qazwini ya rubuta lttafai da dama daga cikisu akwai 


«ایضاحُ الحُجّة فی شرح العُروَة»  «اسلام و فلسفه احکام» و «اسلام و قانون بردگی».


Tags

Ra'ayi