Mar 09, 2016 18:06 UTC

Yau Jumma’a 28 – Esfand-1394 H.SH=08-Jamada-Thani-1437H.K.=18-Maris-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 158 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Maris-1858M. Aka haifi Rudolf Diesel wani injinia dan kasar Jamus, wanda ya kirkiro injin desel a kasar ta Jamus. Desel ya dade yana bincike da gwaje gwaje a kan samarda injin wanda bai amfani da wutan lantarki, yake kuma iya amfani da makamashi mai sauki. Bayan bincike na shekaru masu yawa ya sami nasar kera inji mai amfani da man Desel. Wannan gagarumin aiki na Desl dai ya sauya harkar sifiri a duniya, inda daga bayan ana amfani da “injin diesel” a  manya manyan motoci da jiragen ruwa da sauransu. Kuma har yanzun ana amfani da injuna masu amfani da desel a duk fadin  duniya.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 60 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Jamada-Thani-1377H.K. Aya. Sayyeed Abdul-Husain Saharafudden musawi Amuli ya rasu. An haifi Aya. Amuli a garin Kazimai na kasar Iraqi bayan ya kamala karatunsa na addini a gaban iyaye da manya manyan malamai na lokacin ya koma yankin kudancin kasar Lebanon inda ya ci gaba da karantarwa da kuma wallafe wallafe. Sayyeed Amuli ya yan kasar Lebanon a lokacinda turawan faransa suka shiga kasar don mamayarta. Don haka ya dauki makamai don yakarsu sai dai daga karshe sun fi karfinsa sun kuma tilasta masa hijira zuwa kasar Masar. Daga baya Aya. Amuli ya dawo kasar Lebanon da zama. Inda ya ci gaba da ayyukansa na raya addini. Aya. Sayyeed sharafuddeen Amuli ya rubuta littafai da dama daga cikinsu akwai (al-muraja-aata_ wanda ya kasance muhawarar ne tsakaninsa da shugaban jamai’an al-azhar ta kasar Masar kan halaccin mazhabar shia.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 51 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Maris-1965M. Sarki Faruq tsohon sarkin kasar Masar ya mutu a birnin Roma na kasar Italia. An haifi faruq a shekara 1920 a gidan mahaifinsa sarki Ahmad Fu’ad Pasha. Sannan ya gaji mahaifinsa a kan kujerar sarautar kasar Masar bayan mutuwarsa a shekara 1936M yana dan shekara 16 a duniya. Amma bayan yaki na farko wadanda kasashen larabawa suka yi da sabuwar gwamnatin HKI a kasar Palasdinu a shekara 1948M, kasashen basu sami nasara don haka sai mutanen kasar suka ki shi. A nan ne wasu manya mayan sojojin kasar wadanda suka hada da General Habibu  da kuma Kamal Abdunnasir suka shirya masa juyin mulkin da ba’a zubar da jinni ba a ranar 26-yuni-1952M, inda suka tilasta masa sauka sannan suka dora dansa Ahmad Fu’ad II na wani lokaci kafin su kwace mulki. Daga nan suka kori dangin sarkin daga kasar Masar inda ya koma birnin Roma na kasar Italia da zama har zuwa rasuwarsa a rana irin ta yau.

Tags

Ra'ayi