Mar 09, 2016 18:13 UTC

Yau Asabar 29 – Esfand-1394 H.SH=09-Jamada-Thani-1437H.K.=19-Maris-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 133 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Maris-1883M. aka haifi Sir Norman Haworth wani masanin ilmin kimiyyar sinadarai dan kasar Britania. Sir Haworth ya yi bincike mai yawa kan sinadarin hydrocarboms in da daga karshe ya gano yadda aka ginin haliitarsu yake. Daga cikinsu sir Haworth ya gano molecule na sukari da kuma vitamin c wanda ya sanya wa suna Ascorbic acid. Don irin nasarorin da ya samu na kawo ci gaba a harkokin ilmi sir Norman Haworth ya karbi kyautar Nobel a shekara ta 1937M. Sannan ya rasu a shekara 1950M.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 65 da suka gabata a rana irin ta yau wato 29-Esfand-1395H.SH. Bayan gwagwarmaya na wani lokacin daga karshe Priministan kasar Iran ya sami nasarar samun yardar majalisun wakilai da dattawan kasar Iran kan tabbatar da dokar maida kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar Iran ya zama na kasar. Kafin haka dai turawan Ingila ne suka dukkan wadan nan ayyuka tare da samun goyon bayan sarki sha.
Tabbatar da wannan dokar dai ya zama tubali na farko wanda mutanen kasar Iran musamman malaman addini suka azan a gwagwarmaya da turawa yan mulkin mallaka da kuma sarakuna masu goya masu baya.  Wannan dokar dai ta fara aiki a ranar 29-Khurdod -1330H.SH. Turawan ingila sun ji haushin wannan lamarin, har ya kai ga suka shigar da kara a gaban kotun kasa da kasa, amma kotun ta yanke hukuncin mai goyon bayan iraniyawa.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 52 da suka gabata a rana irin ta yau wato 29-Esfand-1342H.SH.  Imam Khomaini (q) wanda ya assasa JMI ya bukaci mutanen kasar Iran da su ki yin bukukuwan sabon shekara na iraniyawa wato Noorooz don nuna kiyayyarsu ga sarakunan Pahalawi wadanda suke amfani da wannan bukin wajen neman yardar abokansa Amurkawa da turawa. Mai makon haki Imam ya bukaci mutanen su hada zaman makoki a garuruwansu don nuna rashin amincewarsu da mummunan halin da mutanenn kasar suke ciki. Hakan kuma ya faro , don haka don irin tasirin da wannan fatawar tayi a rana ta biyu ga watan Farvaddeen na sabuwar shekara ta 1342 jami’an tsaron sha suka yi dirar mikiya a kan malaman addini da dalibansu a makarantar fayziyya dake Qum inda suka kasha da dama daga cikinsu suka kuma kama wasu.

Tags

Ra'ayi