Mar 16, 2016 11:13 UTC

Jama’a masu saurare Assalamu alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wanann shiri na Afirka a Mako.

Shirin dai kan yi dubi kan wasu daga cikin muhimman lamurra da suka wakana a nahiyar Afirka, inda za mu duba batun zaben shugaban kasa a jamhuriyar Benin, da kuma wasu batutuwan na daban a wasu kasashen gwargwadon yadda lokaci ya bamu dama, da fatan za a kasance tare da mu.
…………………………………
To bari mu fara da batun zaben shugaban kasa da aka gudanar a cikin wannan mako a kasar Benin, inda ‘yan takara 33 suka kara da juna, inda kusan dukkaninsu suka maida hankali wajen yi wa al’ummar kasar alkawullance magance matsaloli na rashin aikin yi da kuma cin hanci da rashawa, da sauran alkawulla na inganta rayuwar jama’a.
Shugaba Boni yayi dai zai safka daga shugabancin kasar, bayan da kundin tsarin mulkin kasar ya haramta yin ta zarce kan mulki a kasar, yayin da kuma wasu suke gabatar da korafe-korafen cewa an dan samu matsaloli a lokacin zabe, musaman rashin ganin sunayen wasu daga cikin wadanda suka riga suka yi rijista.
Dangane da yadda aka gudanar da zabe baki daya a kasar Benin mun ji ta baki malam Mustapha Kadi daya daga cikin jagororin kungiyoyin farar hula a Nijar, kuma masani kan harkokin siyasar kasashen yammacin Afirka, ga abin da yake cewa.
………………………
A cikin wannan mako ne Allah ya yi wa daya daga cikin cikin fitattun ‘yan siyasa a nahiyar Afirka Dr. Hassan Turabi na kasar Sudan rasuwa yana da shekaru 84 a duniya, wanda kuma ya kasance mai gida shugaban kasar ta Sudan, kafin daga bisani su raba gari.
Dr. Elharun Muhammad, masanin harkokin siyasa ta kasa da kasa daga Nijariya, ya bayyana mana mahangarsa dangane da marigayi Turabi da kuma rawar da ya taka ta fuskar siyasa a Sudan.
………………………………
To har wala yau a wani abun da shi ma ya dauki hankali a Najeriya a wannan mako shi ne batun gargadin da gwamnatin Najeriya ta yi ga masu dauke da makamai da ke ikirarin ballewa daga Najeriya da kuma kafa kasar mai cin gishin kanta ta Biafra.
Kan wannan batun Prof. Musatafa Gwadabe na jami’ar Ahmadu Bello Zaria, masani kan tarihin siyasa, ya yi mana Karin haske kan yadda yake kallon lamarin.
…………………………….
A can J. Nijar kuwa yanzu haka ana cikin shirye-shiryen tunkarar zabe zagaye na biyu ne, inda bangaren jam’iyyar PNDS tarayya ta ce ta shirya zuwa zagaye na biyu tare da dan takararta Muhammad Isufu, kamar yadda Malam Sani Sabo kakakia  jam’iyyar ya sheda
…………………………………………..
To amma ko su nasu bangaren jam’iyyar Lumana tare da sauran bangaren adawa da suke mara baya ga Hama Amadu kowane hali suke ciki, ga dai Karin hasken da Mamman dan buzuwa kakakin jam’iyyar Lumana ta Malam Hama Amadu.
………………………..
To a can kasar Somalia kuwa Amurka ce ta ce ta kai wani hari da jirgi maras matuki a kan wani babban sansani ‘yan kungiyar Alshabab reshen kungiyar alkaida a Somalia da ke dauke da makamai, inda bayanin ma’aikatar tsaron Amurka ya ce an kai harin ne da jirgi maras matuki a kan mayakan kungiyar, inda kimanin 150 daga cikinsu suka rasa rayukansu, kungiyar ta Alshabab dai ba ta komai kan lamarin ba.
To bari mu sake komawa tarayyar Najeriya, daya daga cikin lamurran da jama’a suke tofa albarkacin bakinsu a kansu shi ne batun tsadar kayan abinci, wanda dan rahotonmu a Katsina Zahraddini Umar ya yi mana bita kan hakan daga Katsina.
…………………………..
To jam’a masu saurare lokacin da muke da shi ya kawo jiki a nan zamu dakata sai Allah ya kai mu mako nag aba za a ji mu dauke da wani jigon, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.


Tags

Ra'ayi