Mar 16, 2016 11:20 UTC

Jama’a masu saurare Assalamu alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wanann shiri na Afirka a mako.

Shirin dai kan yi dubi kan wasu daga cikin muhimman batutuwa da suka shafi nahiyar Afirka, a yau shirin zai leka kasashen Ivory Coast, J. Nijar, Nijaeriya, Masar da ma wasu kasashen an daban gwargwadon yadda lokaci ya ba mu hali.
Da fatan za a kasance tare da mu.
……………………………………………….
Bari mu fara daga Ivory Coast, inda a ranar Lahadi da ta gabata ce aka kai wani harin ta’addanci kan wani katafaren otel na Grand Bassam da ke kasar Ivory a kusa da birnin Abijan, inda aka kasha utane 16 da suka hada da soji da kuma fararen hula masu yawon bude id, amma daga bisani jami’an tsaro sun kashe uku daga cikin maharani.
Kungiyar alkaida  a yankin Magrib ta ce ita ce ke da alhakin kaddamar da wannan hari.
Kan wannan batu mun ji ta baki Prof Yusuf Yahaya masani kan harkokin siyasa da tarihi daga jami’ar Yamai, ga dai adda yake kallon wannan lamari.
……………………..
To a can jamhuriyar Nijar kuwa batun zabe zagaye na biyu da za a gudanar a ranar 20 ga wannan wata na Maris da muke ciki shi ne ke ci gaba da daukar hankula, musamman ma batun kin amincewa da bukatar lauyoyin daya daga cikin ‘yan takarar na bangaren adawa malam Hama Amadou kan bayar belin dinsa o kuma yi masa sakin talala.
Alh. Muhammad Lawali Lege shi ne kakakin jam’iyyar Lumana ta Hama Amadu, ko yaya suke kallon wannan mataki na kotu? Ga Karin hasken da ya yi wa sashen Hausa.
………………………………
To su anasu bangaren jam’iyyar PDNS tarayya mai mulki ko wane shiri suke ciki kan wannan zabe, ga abin da Ahmad Rufai Chopa kusa a jam’iyyar yake cewa.
………………………….
To su ma a nasu bangaren kungiyar malaman addinin musluci na kasa a j. Nijar sun yi kira ga al’ummar kasar dangane da muhimamncin gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, ga dai kiran da kungiyar malaman addinin ta yi.
………………………….
Tarayyar Najeriya kuwa wani abu wanda ya dauki hankai matuka a kasar a cikin wannan mako shi ne rikicin da ya barke a birnin Lagos, inda aka kashe mutane da dama, da bata dukiyoyi masu tarin yawa musamman a kasuwar Mile 12 da ake kai kayan gwari. Malam Yunus mazaunin birnin lagos ne, ya kuma yi wa sashin Hausa Karin bayani kana bin da ya gane ma idanunsa.
……………………………..
To wani batun wanda shi ma har yanzu yana ci gaba da daukar hankali shi ne batun wawure kudaden sayaen makamai a lokacin gwamnatin da ta gabata, inda har yanzu ake ci gaba da bankado mutanen da suke da hannu wajen cinye kudaden.
Dan majalisar dattijan Najeriya Sanata Sulaiman nazifi, ya bayyana ma dan rahotonmu a Abuja Muhammad sani Abubakar matsayinsu kan batun.
………………………….
A can kasar Liberia kuwa, wata sabuwar kwaskwarima da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar , ta bayar da shawara kan cewa, a mayar da addinin kirisanci ya zama shi ne addinin kasa  a hukumance.
Ko shakka babu wannan lamari bai yi wa mabiya addinin muslunci dadi ba, domin ana kallon kasar Liberia  matsyin kasar da babu ruwanta da bin tsarin wani addini, amma wannan mataki zai mayar da kasar ta zama kasar mabiya addinin kirista a hukumance.
Hakan ya sanya musulmi janyewa daga majalisar addinai ta kasar, wadda ta hada manyan addinai biyu na kasar wato kiristanci da musulunci, domin nuna rashin gamsuwarsu da hakan.
Kafin wanann kudiri ya zama doka dai sai alummar kasar sun bayar da ra‘ayinsu a kai. Kiristoci dais u ne masu rinjayea  kasar Liberiya, yayin da musulmi yawansu ya kai kimanin kasha 15% zuwa 20%.
Music…………………………………..
A can kasar Masar kuwa, Sharif Ismail firayi ministan kasar ne ya kori ministan shari’a Ahmad Zind saboda yin kalamin batunci ga manzon Allah (SAW) tare da daukar matakan ladabtarwa akansa.
Ahmed al-Zind ya fada a wata muhawara gidan talabijin inda yake mayar da martani kan kama wani Dan Jarida saboda zargin cewar ya bata masa suna, inda ministan yace koda Mazan Allah (SAW) ne zai kama shi.
Jim kadan bayan yin furuci, ministan ya yi nadama kana bin da ya fada, inda yace yana tuba ga Allah da neman gafara, kamar yadda kuma washe gari ya kara sanar da cewa abin da ya yi babban kure ne kuma yana neman afuwa.
A nasu bangaren manyan alakalan kasar Masar sun fitar da wata sanarwa da ke cewa ba su amince da matakin da aka dauka na korar Ahmad Zind daga mukaminsa ba, domin kuwa abin da ya yi kure ne, kuma ya nemi gafarar ubangiji da al’ummar musulmi, kuma a cewarsu kowa zai iya yin tuntuben harshe wajen Magana.
Furucin dai yana ci gaba da fuskantar kakkausar suka da mayar da martini daga sassa daban-daba na cibiyoyin muslunci a kasar ta Masar da ma sauran kasashen musulmi, tare da yin kira da a dauki kwararan matakai na ladabtarwa a kansa sakamkon yin furuci na batunci ga manzon Allah (ASW)
Kamar yadda kuma wasu suke ganin cewa ya kamat a dauki mataki da ya dace domin hana faruwar irin hakan a kasar ta Masar nan gaba, doin kare martabar manzo.

…………………………….
To jama’a masu saurare lokacin da muke da his ya kawo jiki a nan za mu dasa aya, sai Allah ya hada mu a saduwa ta gaba, kafin lokacin nake yi muku fatan lhairi, wassalmau alaikum wa rahmatullah.

Tags

Ra'ayi