Mar 23, 2016 19:27 UTC

ama’a masu saurare Assalamu Alaikum, barkanku da warhaka barkanmu da sake saduwa da kua cikin wannan shiri na Afirka a mako.

Shirin kan yi dubi kan wasu lamurra da suka shafi wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka, a yau ma da yardar Allah za mu leka J. Nijar domin jin batun zabe zagaye na biyu, da kuma tarayyar Nijeriya da ma wasu kasashen gwargwadon yadda lokaci ya ba mu hali, da fatan za a kasance tare da mu.
……………………………….
To madalla bari mu fara da batun zaben shugaban kasa zagaye na biyu da ya gudana a J. Nijar a cikin wannan mako, wanda shugaban kasar mai barin gado Muhammad Yusuf ya kara da dan karar bangaren adawa Hama Amadu, duk kuwa da cewa Hama da sauran bangaren adawa sun ce sun janye wa zaben, saboda dalilan da suka bayyana, daga ciki kuwa har da cewa a zabe zagaye na farko an tafka magudi, haka nan kuma an muzgunawa dan takararsu Hama Amadu.
To bari mu ji ta bakin shugaban jam’iyyar PNDS tarayya mai mulki Bazum Muhammad abin ya bayyana bayan jefa kuri’arsa.
Mosahebeh (1) ……………………………..
Dangane da zaben dan rahotonmu a Damagara Musa Malam Sule ya ji ra’ayoyin mutane kan zaben.
Mosahebeh (2) …………………………………
To a can jahar Maradi ma bayan da ya jefa kuri’arsa gwamnan jahar Abdu Mamman ya sheda cewa.
Mosahebeh (3) …………………………………………
Shi ma a nasa bangaren Abdu Dan Neto jami’I na hukumar zabe ta CENI ya yi bayani kan yanayin zaben zagaye na biyu.
Mosahebeh (4)…………………………….
To su jama’a a jahar Maradin sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan zabe, inda mutane suke da ra’ayoyi mabanbanta kan wannan zabe, tsakanin masu goyon baya da kuma masu kaurace masa.
Mosahebeh (5) ………………………………….
A can jahar Agadez kuwa dan rahotonmu Umaru Sani ya yi mana bita kan yadda zaben ya gudana a fadin jahar.
Mosahebeh (6) …………………………………….
To baya ga jamhuriyar ar nar Lahadi 20 ga wannan wata na Maris an gudanar da zaben shugaban kasa  zagaye na biyu a wasu kasashe na Afirka, da suka hada da Congo-Brazzaville,   Benin, Zanziba, a Cape Verde kuwa zaben 'yan majalisar dokoki aaka gudanar.
'Yan Senegal kuwa na kada kuri'ar raba gardama ne na amincewa da wasu sauye-sauye a kundin tsarin mulkin kasar, ciki har da rage wa'adin shugabancin kasar.

…………………………………………………

A tarayyar Najeriya kuwa batun matsalolin da ‘yan gudun hijira suke fuskanta yankunan arewa maso gabashin kasar, na ci gaba da daukar hankula, inda ake ci gaba da yin kira ga mahukunta da su kara kaimi wajen agaza wa wadannan bayin Allah. Hajiya Kellu Gujba, tsohuwar mai baiwa gwamnan jahar Yobe shawara ce kan harkokin lafiya, kuma mai fafutuka kan lamurra da suka shafi mata, ta bayyana mahangarta kan matsalolin da ‘yan gudun hijirar suke ciki da kuma irin bukatun da suke da su musamman ma dai mata daga cikinsu, a zantawarta da dan rahotonmu Mu’azu Umar Haradawa.
Mosahebeh (7)……………………………
To har wala yau kan batun matsalolin ‘yan gudun hijirar da ma mutanen da suke fuskantar matsaloli makamantan hakan a yankunan arewacin Najeriya baki daya, an gudanar da wani zaman taro wanda ya hada kungiyoyin kare hakkin bil adama, na bayar da agajin gaggawa, da na likitoci da sauransu, domin samo bakin zaren warware wadannan matsaloli da kuma yadda a za a fuskance su. Muhammad Nuradden Lemu daga Jahar Niger na daga cikin mahalarta taron, ga kuma Karin hasken da ya yi wa sashen Hausa.
Mosahebeh (8) …………………………………..
 A kasar Kamaru kuwa a cikin wannan mako ne aka yanke hukunci kan wasu ‘yan kungiyar Boko Haram da jami’an tsaron kasar suka cafke, a kan haka muka ji ta bakin Major Yahya Shinko mai ritaya masani kan harkokin tsaro a Najeriya, kan yadda yak ekallon wannan mataki da kuma tasirinsa, musamam a kasashen ad suke fama da wannan matsala ta Boko Haram.
Mosahbeh (9)………………………


 To jama’a masu saurare da wannan muka kawo karshen shirin sai Allah ya kai mu mako nag aba za a ji mu dauke da wani jigon, kafin lokacin muke muku fatan alkhairi.

Tags

Ra'ayi