Mar 03, 2018 16:00 UTC

Yau Lahadi 20-Esfand-1396H.Sh=22-J-Thani-1439H.K=11-Maris-2018M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 33 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Maris-1985M. Aka zabi Milkhail Gorbachev, a matsayin shugaban tarayyar Soviet, duk da cewa shi ne mafi karancin shekaru a majalisar koli ta jam'iyyar gurguzu ta tarayyar Soviet. Bayan karbar madafun iko Gorbachev ya fara gabatar da sauye sauye masu muhimmanci a kasar wadanda ya kai ga bayan shekaru 6 tsarin gurguzu ta wargaje a tarayyar ta Soviet. Sojojin tarayyar Soviet sun yi kokarin yi masa juyin mulki a cikin watan Augustan shekara ta 1991. Amma ba tare da samun nasara ba. Tarayyar Soviet ta wargaje ne a cikin watan Decemban shekara ta 1991.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 14 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Maris-2004M. Wasu boma- bomai masu karfin gaske guda 5 sun tashi a cikin wasu tashoshin jiragen kasa na karkashin kasa, wanda ake kira Metro a birnin Madrid na kasar Espania. Hare-haren sun kashe mutane akalla 200 sannan wasu 1000 guda suka ji rauni. Gwamnatin kasar Espania ta lokacin dai ta dora laifin wannan aikin kan yayan kungiyar Eta masu son bellewa daga kasar. Amma kungiyar yan ta'adda ta Al'qaeda a wata sanarwan da ta fitar ta dauki alhakin tada boma boman. Wadannan hare-hare sun jawo sauyin gwamnati a kasar ta Espaniya makonnin kadan bayan hare-hare, sannan kasar Espania ta janye sojojinta daga kasar Iraqi.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 12 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Maris-2006M. Tsohon shugaban kasar Ugoslaviya Slobodan Mulisovic ya mutu a cikin kurkuku a birnin Hek yana dan shekara 64 a duniya. A shekara ta 2001 ne Milosovic ya shiga hannun kotun kasa da kasa da ke birni Hek don fuskantar zargin kisan kiyashi a lokacin mulkinsa. Ya zama shugaban kasar Ugoslaviya a shekara ta 1989. Amma bayan bellewar kasar Bosnia daga tarayyar Ugoslaviya, bayan wani zaben raba gardama da aka gudanar a yankin, Milosovic ya ingiza sabiyawan bosnia suka yiwa al-ummar musilmin Bosniya kisan kiyashi wanda ya lakume rayukan musulmi dubu 250, sannan wasu miliyon daya da raba suka yo huijra. An fara sauraron shari'ar milosovic a shekara ta 2002 kafin mutuwarsa.

 

Tags

Ra'ayi