Mar 05, 2018 08:12 UTC

Yau Talata 22-Esfand-1396H.Sh=24-J-Thani-1439H.K=13-Maris-2018M

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 895 da suka gabata a rana irin ta yau wato 24-J-Thani-544H.K. Aka haifi Ahmad bin Ali Baihaki babban malamin addini masanin ilmin karatun Alkur'ani mai girma a garin Nishabur. Da farki Baihaki ya fara karatun ilmin harshe da ka'idojinsa sannan ya sami korewa a karatu da sanin ilmin alkur'ani mai girma. Baihaki ya rubuta litattafai da dama daga cikinsu akwai "Tajul Masadir" inda ya tattara ilmi mai yawa da ya shafi Alkur'ani mai girma.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 70 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Maris-1948M. Wasu yahudawan sahyoniyya yayan kungiyar yan ta'ada ta Hagono sun kai farmaki kan wani kauyen Palasdinawa da ake kira Husainiya a arewacin Jalil suka yi masu kisan kiyashi. Suka rusa gidajensu. Palasadinawa 602 ne suka yi shahada a wannan harin. Yahudawan sun tsananta kisan Palasdinawa a lokacin ne don su sami damar shelanta kafuwar haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin watan Mayu mai zuwa na wancan shekara.

03-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 38 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Esfand-1358H.SH. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa JMI ya bada umurnin kafa wata hukuma wacce zata kula da iyalan shahidan juyin juya halin musulunci a kasar. A cikin umurnin Imam yana cewa "Ko wa daga cikinmu ya san cewa mutane daga bangarori daban daban sun taimaka wajen samun nasarar juyin juya halin musulunci a wannan kasar, amma nag aba-gaba daga cikinsu su ne shahidai da kuma wadanda aka gurgurta rayuwarsu sanadiyyar wannan gwagwarmayan. Don haka dole ne a kafa wata hukuma wacce zata dauki nauyin iyalan dukkan shahidai da kuma wadanda aka gurgurta rayuwarsu. Da wannan umurnin ne aka kafa "Mu'assara Shahidai a nan kasar Iran " wacce take daukar daunin iyalan shahidai da kuma wadanda suka gurgunce saboda yaki da kuma gwagwarmayan kafin nasara.

 

Tags

Ra'ayi