Mar 05, 2018 08:23 UTC

Yau Lahadi 27-Esfand-1396H.Sh=29-J-Thani-1439H.K=18-Maris-2018M

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 160  da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Maris-1858M. An haifi Rudolf Diesel, wani injiniya dan kasar Jamus wanda ya kirkiri injin Deisel. Kafin haka dai Deisel ya fara bincike kan wanta na'ura wacce zata yi amfani da makamashi mai saiki. A kan wannan kudurin ne Deisel ya sami nasara kirkiro Injin Deisel wanda aka sanyawa sunansa. Injin Seusel dai ya kawo ci gaban sosai a bangaren masana'antu da kuma sifiri a duk fadin duniya kuma har yanzun ana amfani da wannan fasatar tasa. Deusel ya rasu a shelara ta 1313M yana san shekara 55 a duniya.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 56 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Maris-1962M. Masu gwagwarmaya da turawan Faransa yan mulkin mallaka a kasar Algeria bayan bada shahidai kimani miliyon guda sun kai ga nasara. Bayan yaki na shekaru 8 turawan sun amince su bawa mutanen kasar Algeria 'yencin kai a wani taron da aka gudanar a Uryon, bayan samun 'yencin Ahmad bin Bilal ne ya zama shugaban kasar ta Algeria na farko.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 53 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Maris-1965M. Tsohon sarkin kasar Masar Sarki Faruq ya rasu. An haife shi a shekara 1920. Sannan bayan mutuwar mahaifinsa a shelara ta 1936 ya gaji mahifin nasa yana dan shekara 16 a duniya. Bayan yaki na farko tsakanin HKI da kasashen Larabawa, wanda kuma basu sami nasara a cikinsa ba, wasu sojojin kasar suka yi masa juyin mulki suka dora sansa na wani lokaci sannan suka kwace iko da kasar gaba daya a ranar 26-Yulin-1952. Sai kuma a ranar 18-Jenerun -1953 suka tilasta masa gudun hijira a kasashen waje. Faruk ya koma kasar Italia da zama, har zuwa rasuwarsa a rana irin ta yau a shekara ta 1965 yana dan shekara 45 a duniya.

 

Tags

Ra'ayi