Mar 05, 2018 18:19 UTC

Yau Talata 29-Esfand-1396H.Sh=02-Rajab-1439H.K=20-Maris-2018M

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru  999 da suka gabata a rana irin ta yau wato 02-Rajab-440H.K. Abu Raihan Biruni, masanin ilmin taurari, ilmin magunguna da kuma ilmin dabi'a ya rasu. An haifi Biruni a garin Gazne na kasar Afganistana a halin yanzu. Ya tashi yana matukar sun karatu, don haka a cikin dan karamin lokaci ya zama babban malami a cikin fannonon ilmi da dama. Abu raihan ne ya fara gano cewa duniyarmu tana zagaya kanta sau daya a ko wace rana sannan tana zagaya rana a cikin shekara guda. Biruni ya rubuta litatafai da dama daga cikinsu akwai Al-Jawahir.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 291 da suka gabata a rana irin ta yau wato 20-Maris-1727M. Ishaq Newton masanin ilmin lissafi da kuma kimiyar lissafi san kasar Ingila ya rasu. An haifi Newton a ranar 25 ga watan Decemban shekara ya 1642M a kasar Britania. Newton ya shiga jami'a yana dan shekara 18 a duniya. Sannan yana dan shekara 26 a duniya ya zama malamim lissadfi a jami'an Cambrage. Newton ya gano abubuwa da dana a cikin ilmin kimiyar lissafi daga cikinsu ya gano abinda ake kira gravity ko kuma jazibiyya na kasa. Wato kasa na jan kome zuwa jikinsa kamar koran karfe. Newton ya rasu yana dn shekara 84 a duniya a shekara 1727M.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 54 da suka gabata a rana irin ta yau wato 29-Esfanda-1342H.SH. Imam Khomaini (q) wnda ya assasa JMI ya gabatar da wani jawabi mai zafi inda ya yi suka ga shirin da sarki sha yayi na kashe kudade masu yawa saboda bukukuwan idin Nerus ko sabon shekara Iraniyawa. A jawabin nasa Imam ya ce mutane su dauki ranar nerus a matsayin ranar bakin cike a lokacin. Don haka ne ma aka harhada zaman makoki a wurare da dama. Amma a ranar 3 ga watan Farvaddin jami'an tsaron sarki sha sun farwa daliban hauza a Qom suka kuma kashe da dama daga cikinsu.

 

Tags

Ra'ayi