Feb 07, 2016 09:21 UTC
  • Muhimmancin Ilimi Da Tarbiyyar Yara Da Matasa

A shirinmu da ya gabata mun fara gabatar da shimfida ce dangane da muhimman hanyoyin tarbiyya da zamu yi kokarin bijiro da su tun daga matakin yaranta har zuwa samarta musamman a mahangar addinin Musulunci a cikin wannan dan gajeren shirin da zamu gabatar muku na “Yara Manyan Gobe”, sai lokaci ya yi mana halinsa. Don haka a cikin gamonmu na yau zamu yi kokarin kammala shimfidar, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:-

Hakika addinin Musulunci yana da tsari da manufa a dukkanin bangarorin rayuwa da suka hada da al’ada, siyasa, zamantakewa, tattalin arziki da kyawawan dabi’u da sauransu. Haka nan tsarin tarbiyya yana daya daga cikin tsari mai muhimmanci a Musulunci a bangaren rayuwar zamantakewar jama’a da na kadaitaka. Saboda a karkashin koyarwar Musulunci batun tarbiyya yana da matsayi madaukaki da kima.


Sheikh Shahid Murtadha Motahari shahararren masani mai zurfin bincike dan kasar Iran yana da akidar cewa: Musulunci addini ne da ya kunshi dukkanin bangarorin rayuwa, kuma ba tare da nuna bambanci ba ya shimfida hanyoyin shiryar da dukkanin jinsin bil-Adama. Wannan shahararren masanin ilimin falsafa dan kasar Iran ya kara da cewa: Tarbiyya a matsayinta na wani bangaren addinin Musulunci tana da yalwar da za a iya gudanar da bincike mai fadi a cikinta, yana mai jaddada cewa: Tabbas a Musulunci akwai tsarin koyarwa ta musamman yana mai fayyace maganarsa da cewa:-
“Ilimantarwa da tarbiya fannin ilimi ne da ke gina rayuwar mutum, kuma makaranta ne da ke kunshe da manufofi kebantattu da suka hada dukkanin bangarorin rayuwa, misalin tsarin kare hakkoki, tattalin arziki da siyasa, kai babu wani bangaren rayuwa da babu tsari na musamman a kansa”.
A cikin ayoyi da dama na alkur’ani mai tsarki; Tarbiyya tana da matsayi mai girma, kamar yadda ayoyi farko da aka saukar ga Annabi rahama Manzon tsira Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} suke dauke da koyarwa da kuma tarbiyya, inda Allah Madaukaki ke bayyana cewa:-


“Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda ya yi halitta”.
“Ya halicci mutum daga gudan jini”.
“Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne mafi girma”.
“Wannan da ya sanar –da mutum- ta hanyar alƙalami”.
“Ya sanar da mutum abin da bai sani ba”.


Har ila yau ya zo cikin ayoyin Suratus-Sham cewa: Ran mutum yana karbar tarbiyya, kuma shiriyar dan Adam ta dogara ce kan irin kokarinsa. Allah Madaukaki yana cewa: “Hakika wanda ya tsarkake ta –wato rai- ya rabauta. Kuma lallai wanda ya turbuɗe ta –da laifi- ya tabe”.   
Hakika addinin Musulunci ya jaddada muhimmancin tarbiyar dan Adam. Saboda a karkashin kyakkyawar tarbiyya da ladabtarwa ta kyarai; Yara zasu tashi da ladabi da biyayya gami da sanin ya kamata, inda rayuwarsu zata kasance mai amfanarwa tare da watsuwar jin kai, taimakekkeniya da kula da hakkokin da suka rataya a wuyarsu a dukkanin bangarorin rayuwa.  Ya zo cikin hadisin Manzon Allah da na iyalan gidansa tsarkaka {a.s} dangane da muhimmancin tarbiyyar dan Adam cewa: “Mutane kamar ma’adani ne – suna da sabani- akwai dan asali da jebu, -kuma kowane da irin tasirinsa -, kuma mummunar tarbiyya ita ce tushen mummunar dabi’a”.


Tabbas addinin Musulunci a fagen tarbiyya ya buga babban misali cikakke da zai kai mutum ga tsira duniya da lahira, daga cikin misalan da ya shimfida mana akwai fiyayyen halitta Manzon Allah {s.a.w} da jagororin shiriya na iyalan gidansa tsarkaka {a.s} gami da dukkanin Annabawa da Manzanni da Allah ya aiko domin shiryar da al’umma, kuma daga cikin babbar manufa da dalilan aikosu da sakon shiriya shi ne tarbiyantar da mutane tare da tsarkake su daga duk wata daudar rayuwa.


Imam Khomeini da ya jagoranci kafa daular Musulunci a kasar Iran {Yardan Allah ya tabbata a gare shi} yana cewa:-
“Dukkanin tunanin Annabawa da gwagwarmayar da suka gudanar a aikace; a kan kokarin yantar da mutum ne ta hanyar tarbiyantar da shi. Hakika sun zo ne su daga martabar mutum daga matsayinsa na dabi’a zuwa ga matsayi sama da na dabi’a”.


A fili yake cewa: DukkaninAnnabawan Allah {s.a.w} da jagororin shiriya na iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka {a.s} baya ga gwagwarmayar isar da sakon da aka aiko su da shi da kokarin shiryar da mutane, sun kuma zage dantse a fagen tsarkake zukatansu da nisantar duk wata mummunar dabi’a da kuma aikata duk wani kyakkyawan hali lamarin da ya kai su ga babban matsayi da mataki na cika da kamala a rayuwarsu. Hakika wannan babban haske da suka samu ya haskaka rayuwar mutane, don haka gaska su tare da rungumar tafarkinsu lamari ne da zai kai mutum ga babban rabo da cikan kamala duniya da lahira.


Manzon tsira Annabin Rahama Muhammadu dan Abdullahi da ya kasance cikamakin Annabawa {s.a.w} tun daga aiko shi da sakon shiriya har zuwa wafatinsa ya dukufa ne a fagen tarbiyyan al’umma. Tabbas tsananin buri da kaunar Manzon Allah na ganin ya shiryar da mutane tare da dora su a kan kyakkyawar dabi’a sun kai ga rashin shiriyarsu da gurbatar tarbiyyarsu sun fi cutar da shi a kan komai. Hakika kaifin basira da tsananin lura da kuma hikima da Manzon Allah {s.a.w} ya sanya a fagen ganin ya shiryar da mutane tare da tarbiyantar da su kyawawan dabi’u ya sanya a cikin dan gajeren lokaci ya samu gagarumar nasarar janyo hankula jama’a a ciki da wajen Jazirar Larabawa zuwa ga addinin Musulunci tare da rungumarsa hannu biyu-biyu a matsayin hanyar rayuwa gare su. Sakamakon haka ne a cikin dan gajeren lokaci koyarwar addinin Musulunci ta watsa a tsakanin al’umma, musulmi suka zame suna gudanar da addinisu cikin ‘yanci da walwala, kuma wata babbar nasara ita ce kyawawan dabi’un Manzon Allah da na iyalan gidansa tsarkaka {a.s} suka zame fitila da suke haskaka hanyar rayuwar mutane.  


Ra'ayi