Feb 07, 2016 09:34 UTC
  • Muhimman Hanyoyin Tarbiyyar Yara

Masu saurare barkanku da warhaka, kuma barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirinmu na “Yara manyan gobe”. Shirin da a cikinsa zamu yi kokarin bijiro muku da muhimman hanyoyin tarbiyya tun daga matakin yaranta har zuwa samartaka musamman a mahangar addinin Musulunci.

Idan za a iya tunawa a shirinmu da ya gabata muka bijiro muku da kadan ne daga cikin mahangar masana ilimin halayyar dan Adam da na masana ilimin zamantakewa gami da mahangar manyan malaman addinin Musulunci musamman manazarta kan ilimin falsafa da zamantakewa a matsayin shimfida. To a shirinmu na wannan mako zamu shiga cikin kwaryar shirin ne ta hanyar fara gabatar muku da shimfida kan tubalin tarbiyyan yara musamman kafin haihuwarsu, wato tun daga lokacin da suke jarirai a cikin mahaifansu, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa.


Hakika a wannan zamani mafi yawan ma’aurata musamman matasa daga cikinsu, wata tambaya tana bijiro musu kamar haka: Daga wani lokaci ne ya dace su fara gudanar da tarbiyyar yaransu, domin su kasance yara nagari masu tarbiyya a rayuwarsu? Wasu manazarta sun amsa wannan tambayar da cewa: Lokacin tarbiyyar yara yana farawa ne tun daga shekaru shida zuwa bakwai. Wasu kuma suka ce; tun daga lokacin haihuwar yaro ya kamata a fara gudanar da tarbiyyarsa. Yayin da wasu masanan ke bayyana cewa: Tarbiyya tana farawa ce tun tsawon shekaru kafin aure. Kan haka daya daga cikin masana ilimin halayyar dan Adam ke cewa: An tambayi wani masani hikima cewa; Daga wani lokaci ne ya dace a fara gudanar da tarbiyyar yara? Sai Masanin ke amsawa da cewa: “Tun daga shekaru ashirin kafin haihuwar yaro, kuma idan har ba a cimma nasarar bai wa yaron cikakkiyar tarbiyyar da ta dace ba, to ke nan ya bayyana cewa tun shekaru fiye da ashirin kafin haihuwar ya dace a fara gudanar da tarbiyyar”.


Hakika manufar maganar wannan masanin hikima ita ce; Dole ne tun kafin ma’aurata su kai ga samun yaro, su kasance sun dauki matakin tarbiyyar kansu tare da kokarin tsarkake rayuwarsu daga duk wata mummunar dabi’a saboda su samu damar tarbiyantar da yaron da zasu haifa tare da dora shi a kan ingantacciyar turbar rayuwa.


Tabbas a karkashin koyarwar addinin Musulunci batun tarbiyya da ilimantar da yara lamari ne da ke bukatar shimfida da tsari na musamman tun kafin haihuwar yaran, kai tun kafin ma a kai ga yin aure. Saboda ya zo cikin hadisan Manzon Allah da na Iyalan gidansa tsarkaka {a.s} cewa: Tarbiyyar yaro tana farawa ne tun kafin zuwansa duniya wato tun daga lokacin zabar irin macen da ta dace a aura wadda zata kasance mahaifiyar yaron. Tabbas zabar mace tagari mai tarbiyya shi ne matakin farko na samar da yaro da zai kasance mai dauke da siffofin cika da kamala a rayuwa, kuma wannan shi ne tushen samar da iyali na gari mai karko.


A filin yake cewa; Miji da mata sune tushen samar da iyali, sakamakon haka idan har aka samu mahaifa mace da miji masu cikan hankali da zurfin tunani da kuma tarbiyya, hakika an samu kyakkyawar shimfidar tarbiyyar yara. Manzon Tsira da iyalan gidansa tsarkaka {a.s} sun yi wasici kan zurfafa tunani wajen zabar macen aure, inda Manzon Rahama Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} ke bayyana cewa: “Ku auri matan da suke daidai matsayinku, kuma ku auri mata daidai da ku, sannan ku zabawa maniyinku wajen da ya dace”. wato macen da ta dace ta zame uwar ‘ya’yanku.

Hakika Manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka {a.s} sun kasance suna zurfafa tunani kan irin matar da zasu aura da kuma irin mazan da suka dace su auri ‘ya’yayensu mata. An ruwaito cewa: A lokacin auren Sayyidah Fatimah ‘yan Manzon Allah {s.a.w} mutane da dama sun zo neman aurenta kuma a kan manufa da dalilai masu yawa, amma sai Manzon Tsira Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} ya bayyana musu cewa yana jiran hukuncin Ubangiji kan aurenta. Sakamakon haka babu wani da Manzon Allah {s.a.w} ya amince da shi a tsakanin manema Sayyidah Fatimah {a.s}, amma a lokacin da dan Baffansa Ali dan Abi-Talib {a.s} ya zo neman aurenta, sai Annabin Rahama ya yi murmushi ya ce masa: “Ya kai Ali, hakika kafin zuwanka wasu da dama sun zo neman auren Fatimah, kuma na sanar da ita bukatunsu amma sai rashin amincewarta ya bayyana a fuskarta, don haka jira Ni, sai Manzon Allah {s.a.w} ya shiga gida, kuma ya gabatar da sakon dan Baffansa Ali dan Abu-Talib ga ‘yarsa Fatimah, sai ta yi shiru, sai Manzon Allah ya fahimci amincewarta da yardarta a fuskarta, don haka cikin farin ciki Annabin Rahama ya furta kalmar kabbara cewa: Allah Mai Girma yana mai cewa: “Shirun Zahrah alamar yardarta ce”.


Hakika Ali da Fatima sun dace da juna, kamar haka ne Manzon Allah {s.a.w} ke cewa Ummu Ayman: “Ina rantsuwa da Allah na aurar da ‘ya ta ce ga wanda ya dace da ita, mutumin da yake da daukakan matsayi duniya da lahira kuma mutumin da yake da makusancin matsayi a wajen Allah”. Har ila yau yana daga cikin muhimmin hanyar zabar matan aure a tafarkin iyalan gidan Manzon Allah {s.a.w}; Samun mace mai tarbiyya. Tabbas samun daidaiton matsayi a fuskar tarbiyya tsakanin miji da mata yana daga cikin hanyoyin karfafa fahimtar juna a tsakaninsu tare da samun tsarin rayuwar iyali mai inganci, kuma hakan yana daga cikin tubalin samar da ingantacciyar hanyar tarbiyyar yara. Kamar yadda rashin samun fahimtar juna tsakanin miji da mata zai haifar da sabani da husuma a rayuwarsu ta zamantakewa lamarin da zai dishe hasken tarbiyyar yaransu tare da gurbatar tunanin yaran.


Hakika a karkashin koyarwar Musulunci ana lura da daidaiton matsayi a fuskar tarbiyya tsakanin miji da mace da fahimtar juna a tsakaninsu gami da sauran bangarorin rayuwa da suka hada da kyakkyawar dabi’a, kamun kai da tarbiyyar ‘ya mace. Husain Basshar Alwa’sid daya daga cikin sahabban Imam Ali Arridha {a.s} yana ce masa: Wani daga cikin makusanta na yana neman auren ‘ya ta, amma yana da munanan dabi’u, Sai Imam Ridha ya ce masa: “Idan har yana da munanan dabi’u, to kada ka aurar masa da ‘yarka”.


Ra'ayi