Feb 07, 2016 14:14 UTC
  • Muhimman Hanyoyin Tarbiyyar Yara {2}

A shirinmu da ya gabata mun fara gabatar muku da shimfida ce kan tubalin tarbiyyan yara musamman kafin haihuwarsu, wato tun daga lokacin da suke jarirai a cikin mahaifansu, inda muka fara da bijiro muku da wasu daga cikin ra’ayoyin masana da manazarta kan ilimin tarbiyya, sannan muka karfafa maganganunsu da mahangar addini musamman ta hanyar bijiro da hadisa, amma kafin karkare shirin sai lokaci ya yi mana halinsa, don haka a yau zamu kammala bahasin, kamar haka:-

Hakika daukar matakin gudanar da zabe kan matar da mutum zai aura, ya fi muhimmanci a kan gudanar da zabe kan mijin da mace zata aura a fuskar tarbiyya, saboda mace tafi yin tasiri a kan dan da ta haifa fiye da mahaifinsa. Manzon Tsira Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} dangane da zabar macen aure yana cewa: “Ka yi dubi a ina zaka ajiye zuriyarka, saboda tushen iyalai yana tasiri kan yaro”. Har ila yau a wata ruwayar Manzon Rahama{s.a.w} ya fayyace muhimmancin zabar matar da za a aura yana mai bayyana cewa: “Ku nema wa maniyinku wajen da ya dace, kuma ku zabi mace ta gari”.


Haka zalika yana daga cikin hanyoyin tarbiyya, kamar yadda ya zo cikin hadisan Manzon Tsira Muhammadu  dan Abdullahi da iyalan gidansa tsarkaka {a.s}; samun kyakkyawar alaka da fahimtar juna gami da soyayya mai karfi tsakanin ma’aurata wato miji da mata. Hakika samun kyakkyawar alaka tsakanin ma’aurata wata babbar shimfida ce mai karko ta dora yaran da zasu haifa a kan ingantaciyar tubalin tarbiyya, inda yara zasu zame masu koyi da dabi’un mahaifansu tare da mutunta su gami da tasirantuwa da tarbiyyarsu da kuma yin biyayya a gare su, kuma hakan zai yi gagarumin tasiri a tunanin yara, inda a lokacin da suka kai ga matakin aure zasu gudanar da kyakkyawar ma’amala da abokan zamansu na aure kamar yadda suka gani daga mahaifansu.


Har ila yau koyarwar addini da kyawawan dabi’u a fagen rayuwar ma’aurata suna daga cikin muhimman al’amuran da suke yin tasiri a fagen tarbiyyar yara. Hakika duk irin tasirin da addini da kyawawan dabi’u suka yi a lokacin rayuwar yara, to gwargwadon wannan tasirin ne koyarwar ta addini da kyawawan dabi’un da suka koya zasu yi tasiri a rayuwarsu a lokacin da suka girma suka mallaki hankalinsu.


Binciken ilimi yana nuni da cewa: Irin mutanen da suke son samun mata daidai da dabi’ar rayuwarsu, a mafi yawan lokaci sune mutanen da suke gina tunaninsu a kan tubali na akidar addini, al’ada, salon rayuwar iyali da tasirin zamantakewar al’ummunsu. Hakika tsarin rayuwar iyali mai inganci shi ne tsarin rayuwa da ya ginu a kan tubali na kyawawan dabi’u, akidar addini da ingantaccen tsarin zamantakewar al’umma wadanda suke ci gaba da gudana zamani zuwa zamani, tabbas irin wannan tsarin rayuwar iyali shi ne ke kunshe da kyakkyawar tarbiyya da fahimtar juna tsakanin iyalai.


Babu shakka mafi muhimmancin tubalin aure da tafarkin gudanar da rayuwar aure mai karko shi ne wanda aka gina shi a kan mahangar addini kuma ma’aurata suka kasance suna gudanar da rayuwarsu a kan koyarwa da shiryarwar addini da ya zo daga Allah Madaukaki. Dangane da haka Manzon Rahama Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} yake fayyace cewa: “Duk wanda ya auri mace a kan tubalin addini da imaninta, to Allah Madaukaki zai wadata shi da arzikin duniya”.


Tabbas muhimmanci da wajabcin sanya addini a matsayin ma’aunin zaben macen aure shi ne; ana so ne miji da mata su kasance suna gudanar da rayuwarsu a kan salon rayuwa guda da fahimtar juna a tsakaninsu, inda za a samu daidaiton matsayi a fagen tunaninsu da akidarsu gami da dabi’unsu. Har ila yau mace ma’abuciyar addini a mafi yawan lokaci an fi samun cewa ta fito ce daga zuriya mai tsoron Allah da riko da akida lamarin da zai karfafa ta a kan tsarkin zuciya, kyawawan dabi’u da nisantar munanan ayyuka. Hakika tsarkakar zuriya da riko da addini, su ke yin gagarumar tasiri a fagen tarbiyya tare da dora mutum a kan kyakkyawan tubalin rayuwa mai inganci.


Hakika riko da koyawar addini shi ne babban tubalin tarbiyya da zai taimaka a fagen katange mutum daga gurbatar tunani da afkawa cikin munanan dabi’u masu rusa dan Adamtaka. Tabbas kyakkyawar dabi’a a mahanga ta hankali da shari’a; siffa ce da ake kaunarta, sakamakon haka miji da mata a matsayinsu na tushen iyali, suna bukatar siffantuwa da kyawawan dabi’u a fagen rayuwarsu domin su kasance abin koyi ga ‘ya’yansu, saboda yana daga cikin manyan manufar aiko Annabawa da Manzanni shimfida kyakkyawar dabi’a a bayan kasa.


A fili yake cewa; riko da addini da siffantuwa da kyawawan dabi’u suna taka gagarumar rawa a fagen tarbiyya da dora yara a kan ingantaccen tafarki, saboda a duk lokacin da mahaifa suka kasance masu riko da addini da siffantuwa da kyawawan dabi’u; sun fi nasarar samar da yara nagari masu tarbiyya da zasu amfanar da al’umma.
 

 

 

Ra'ayi