Apr 25, 2016 12:52 UTC

Jama’a masu saurare Asslamu barkanku da warhaka barkanmu da sake saduwa da kua cikin wannan shiri na Afirka a mako, shirin da kan yi dubi akn wasu daga cikin muhimman lamurra da suka wakana a cikin mako a nahiyar Afirka, a yau za mu duba batun rantsar da shugaban Jamhuriyar Nijar, daga na kuma mu leka Nijariya da ma wasu kasashen gwargwadon yadda lokaci ya ba mu hali, da fatan za a kasance tare da mu.

Bari mu fara daga Jamhuriyar Nijar, a cikin wannan mako ne aka rantsar da shugaban kasar Nijar Muhammad Isufu a matsayin shugaban kasa a wani sabon wa’adin mulki na shekaru biyar a kasar, bayan gudanar da zabe gayaye na farko wanda babu ko daya daga cikin ‘yan takara 14 da ya samu nasarar samun kashi 50%, wanda hakan ya sanya a ka gudanar da zaben zagaye na biyu tsakanin Muhammad Isufu da kuma Hama Amadu, duk kuwa da cewa jam’iyyun adawa da suke mara ma Hama baya da shi kansa Hama sun bukaci magoya bayansu da su kaura ce ma zaben.
Dangane batun rantsar da Muhammad Isufu a matsayin shugaban kasa a wa’adin mulki na biyu, Hassan Barka ya yi mana bita takaitacciyar bita kan tarihin shugaban.
……………………..
To a daya bangaren guma shugaba Isufu ya nada Fira minista Birji Rafini da ya kafa sabuwar gwamnati. A kan haka mun ji ta bakin Maina Karte Bukar na kungiyar farar hula, kan yadda yake kallon lamarin.
 ………………………..
To a nasu bangaren ‘yan adawa a kasar ko mene matsayin rantsar da Muhamamd Isufu a matsayin shugaban kasa a wa’adin muki na biyu? Ga abin da kusa a kawancen adawa na COPA Ahmad Risa yake cewa.
 ………………………..
Bari bangaren jama’a a jamhuriyar ta Nijar kan ra’ayoyinsu da kuma fata da suke da ita daga sabuwar gwamnati.
 …………………………
To yanzu kuma bari mu leka tarayyar Najeriya, inda a cikin wannan mako ne shugaban kasar Muhammad Buhari ya bayyana cewa, za su dauki dukkanin matakai da suka dace domin ganin an rage yawan abincin da ake shigowa da shi a cikin Najeriya, tare da kara bunkasa ayyukan samar da abinci a cikin gida, maimakon kashe makudan kudade domin shigowa da shi daga kasashen ketare.
Malam Mahmud jami’i ne a bangaren ayyukan noma da kiwo a Najeriya, ko ya yake ganin mataki?
 …………………………..
To daya bangaren kuma wasu matasa ne da suka fito daga jahohi daban-daban na Najeriya, suka gudanar da wani gangami da jerin gwano a birnin Abuja, domin yin kira da kakausar murya ga shugaba Buhari, kan ya dauki kwararan matakai wajen ganin an magance matsalar da ta addabi Najeriya ta cin hanci da rashawa, inda wasunsu ke cewa akwai wasu na hannan damar shugaba Buhari wadanda su ne suke hana ruwa gudu a kasar.
Dan rahotonmu a Abuja ya ji ta bakin wasu daga cikin matasa  alokacin da suke gudanar da wannan gangami, ga dai abin da suke sheda masa.
…………………….
Daga Najeriya kuma bari mu nufi Gambia, inda ake ci gaba da kai ruwa rana a tsakanin kasar ta Gambia da kuma makwabciyarta Senegal.
Yanzu haka dai gwamnatin kasar Gambia ta kai karar Senegal ga kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS.
Gwamnatin kasar ta Gambia ta zargi Senegal da kokarin yi ma tattalin arzikinta zagon kasa, ta hanyar hana manyan motocin kasarta masu daukar kaya shiga cikin kasar ta Gambia, yayin da kuma kasar Senegal ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamakon kara kudin haraji da kasar ta Gambia ta yi a kan motocin daukar kayan, amma dai za a warware matsalar ta hanyar tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.
………………………………….
Gwamnatin kasar Mali ta sake sabunta dokar ta baci a kasar har tsawon kwanaki 10 a nan gaba.
A wani zaman majalisar ministoci da shugaban kasar ta Mali Ibrahim Bubakar Keita ya jagoranta a jiya abirnin Bamako, an sanar da sake sabunta dokar ta baci a fadin kasar.
Bayanin zaman ya ce har yanzu akwai sauran barazanar ta'addanci a cikin kasar da kuma wasu kasashe masu makwabtaka da kasar, kuma Mali ta dauki wannan batu da matukar muhimmanci.
Gwamnatin kasar Mali ta kafa dokar ta baci ne tun bayan kai harin da aka kai kan wani katafaren otel na Radison da ke birnin Bamako a karashen watan watan Nuwamban shekara ta 2015 da ta gabata.
…………………….
To jama’a masu saurae lokacin da muke da shi ya kawo jiki dole a nan za mu dasa aya sai idan Allah ya kai mu mako nag aba  za a ji mu dauke da wani jigon, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alikum.

 

Tags

Ra'ayi