Apr 27, 2016 15:10 UTC
  • Rainon Ciki Domin Kare Lafiyar Yara {6}

Masu saurare barkanku da warhaka, kuma barkanmu da sake saduwa da ku a ci gaban shirinmu na “Yara manyan gobe”. A shirinmu da ya gabata mun fara bijiro muku da batun rainon ciki ne da matakan da suka dace mahaifiya ta kula da su saboda muhimmancinsu a fagen kare lafiyar jiki da na ruhin yaron da zata haifa gami da gargadi kan nisantar munanan dabi’u ciki har da nisantar cin abincin haram, sai lokaci yayi mana halinsa don haka a cikin shirinmu na yau zamu ci gaba:-

Hakika addinin Musulunci ya jaddada muhimmancin lura tare da tantance tsakanin abincin halal da na haram domin tasirin kowane daga cikinsu a fagen tarbiyya mutum. Ya zo cikin tarihi cewa; Imam Husaini {a.s} yana fayyace dalilin kiyayya da gabar makiyansa a kan iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka {a.s} da cewa: “Sun cikin cikinsu ne da haramun don haka -haram- ya lullube musu zukata, sakamakon haka ba zasu karbi gaskiya ko saurararta ba”.  

Hakika abincin haram yana da mummunan tasiri a kan tsatson mutum. Ayatullahi Mazahiri daga cikin fitattun malaman tarbiyya da kyawawan dabi’u dan kasar Iran yana bayani kan tasirin abinci dacewa: “Hakika abincin halal da ke taimakawa wajen samar da maniyyi yana gagarumin tasiri na ban mamaki a kan kyakkyawar tarbiyyan yaron da za a haifa da wannan maniyyi. Kamar yadda abincin haram yake da mummunan tasiri wajen gurbata tarbiyyan yaron da za a haifa da wannan maniyyi…” Yana mai fayyace cewa; Abincin haram da dukiyar haram sun fi muni a kan duk wata gobara, kuma matukar maniyyin yaro ya samo asali ne daga abincin haram, to lallai shiriyarsa lamari mai cike da tarin matsala”.

An habarto cewa: An ce wa wani mutum bawan Allah mai daraja cewa; Lallai danka baya da tarbiyya! Sai ya ce; mene ne ya aikata? Sai aka ce masa; mai dakon ruwa yana dauke da jakar fata da ake dibar ruwa ciki a kan kafadarsa, yana cikin tafiya, sai danka ya soka allura a jakar fatar lamarin da ya yi sanadiyyar hujewar fatar tare da zubar ruwan da ke ciki. Sai wannan mutum mai daraja ya yi tsananin fushi kuma ya dauki matakin titsiye matarsa, sai matar da shiga cikin damuwa, tace lallai babu mamaki. Cikin mamaki wannan mutum ke cewa; Don mene ne babu mamaki? Sai matar ke cewa; A lokacin da nake dauke da cikinsa na zauna a karkashin wata bishiyar rumman mallaki wasu mutane, bayan da sha’awar rumman din ta kama ni, sai na dauki matakin huda rumman guda da allura inda na sha ruwan ta wannan kafar da na huda. Sakamakon laifin huda rumman din mutane tare da shan ruwanta bada izini ba, shi ne tasirin wannan laifi ya wurga dana cikin wannan mummunar dabi’a ta huda jakar ruwan mutane”.

Daya daga cikin muhimman al’amuran da suke kara gadarwa jariri kwanciyar hankali da nutsuwa a cikin mahaifiyarsa shi ne: Mace mai dauke da juna biyu ta kasance a cikin kwanciyar hankali da nutsuwar ruhi. Hakika matukar mace mai juna biyu tana cikin damuwa da tashin hankali musamman na ruhi, hakan yana yin mummunan tasiri a kan jaririn da ke cikinta musamman a rayuwarsa bayan zuwansa duniya. Wannan fadakarwa tana da tushe a shari’ar Musulunci, kamar yadda bincike na ilimin zamani ya tabbatar da hakan. A bangare guda kuma gwargwadon irin matakin da mace mai juna biyu ta dauka na nisantar ayyukan laifi da munanan dabi’u, to kwatankwacin irin kwanciyar hankali da nutsuwa gami da tsarkin rayuwa da jaririnta da ke cikinta zai samu a rayuwarsa ta nan gaba a bayan haihuwarsa.

Har ila yau daya daga cikin al’amura masu tasiri a fagen gadar da kwanciyar hankali da nutsuwa ga jariri a cikin mahaifiyarsa shi ne; Irin mutanen da mace mai ciki take rayuwa tare da su a karkashin inuwa guda. Gwargwadon irin matakin da mutanen da suke rayuwa da mace mai ciki suka faranta mata rai a irin hirarrakin da suke gudanarwa da ita, kwatankwacin irin kyakkyawar tasirin da hakan zai yi a kan jaririn da ke cikinta. Kamar haka ne idan mace mai dauke da juna biyu tana zama da mutanen banza masu furta munanan maganganu ko take halattar wajajen batsa da alfasha, hakan zai iya yin mummunar tasiri a kan jaririn da ke cikinta a bayan zuwansa duniya.

An ruwaito hadisi daga Manzon Tsira, Annabin Rahama Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} yana bayyana cewa: “Maganganun abokin zama nagari, misalin mai sayar da turare ne, idan har bai yayyafa maka turaren ba, to duk da haka zaka amfana daga kamshin turaren. Haka nan maganganun abokin zama mutumin banza, kamar makeri ne, idan har tartsatsin wutar kirarsa bai kona ka ba, to mummunan warin wutar kirar zai yi tasiri a kanka”.

Sakamakon haka dole ne a kan mace mai juna biyu ta dauki matakin kiyaye hukunce-hukuncen shari’a ta hanyar nisantar ayyukan laifi da suke haramun gwargwadon iyawarta ciki har da furta munanan maganganu da suke matsayin alfasha tare da nisantar da kan ta daga majalisin gulmace-gulmace da yi da mutane.

Hakika matakin gudanar da addu’o’i da zikirin Allah suna da gagarumin tasiri a kan cikan lafiya da amincin jaririn da mace mai juna biyu ke dauke da shi. Tabbas mace mai juna biyu kamar mai jihadi ne a tafarkin Allah da addu’arsa ke saurin karbuwa a wajen Allah Madaukaki. Hakika gudanar da addu’a da neman bukatu a wajen Allah Madaukaki suna daga cikin madaukakin matsayi da ke fayyace kasantuwar mutum a matsayin hakikanin bawa ga Allah, kamar yadda ya zo cikin Suratul-Furqan a aya ta 77 cewa: “Kace; Ubangijina ba zai kula da kuba, ba domin addu’arku ba….”. Sakamakon haka ya zame dole a kan mahaifiya matukar tana bukatar zuriya ta gari da ‘ya’yaye masu kyawawan dabi’u ta kasance ta zage dantse tare da dawwama a kan addu’a da neman kusanci a wajen Allah Madaukaki. Daya daga cikin irin wadannan addu’o’i shi ne kamar yadda ya zo cikin alkur’ani mai girma Suratu-Ali Imrana aya ta 38 cewa: “Ya Ubangiji ka azurta ni daga gare ka zuriya tsarkakekkiya, hakika Kai Mai karbar addu’a ne”.

Har ila yau a cikin Suratul-Furqan aya ta 74 Allah Madaukaki yana cewa: “Kuma waɗanda suke cẽwa "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu sanyin idãnu daga mãtanmu da zũriyarmu, kuma Ka sanya mu abin koyi ga mãsu tsoronka”. Hakika mahaifa miji da mata zasu iya kiyaye irin wadannan addu’o’i da suka zo cikin alkur’ani wajen rokon Allah Madaukaki kan ya azurta su da yara nagari masu koshin lafiya da cikan halitta.


Ra'ayi