Apr 27, 2016 16:05 UTC
  • Tarbiyyan Jariri Bayan Haihuwarsa {2}

Masu saurare barkanku da warhaka, kuma barkanmu da sake saduwa da ku a ci gaban shirinmu na “Yara manyan gobe”. A cikin shirinmu da ya gabata mun fara gabatar muku da batun matakan tarbiyyar jariri ne a bayan zuwarsa duniya, inda muka ambaci wasu daga cikin ladubba masu muhimmanci da suka dace a kiyayesu a bayan haihuwar jariri, sai lokaci yayi mana halinsa, don haka a yau zamu ci gaba, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:-

Hakika mun bayyana cewa; Kyakkyawar suna mai ma’ana da mahaifa zasu radawa jaririn da suka Haifa musamman sunar da ta samo asali daga kyakkyawar siffa ko dan Adamtaka, hakan yana gagarumin tasiri a fagen rayuwar jaririn da aka haifa a tsawon rayuwarsa musamman idan mahaifan suka dauki matakin tarbiyyantar da jaririnsu a kan siffantuwa da wannan kyakkyawar siffar da sunansa ta kunsa. A bangare guda kuma idan mahaifa suka dauki matakin sanya wa jaririnsu mummunar suna da bata dace ba, nan ma wannan sunar tana tasiri a kan jaririn da suka haifa. A wasu lokuta ma munanan sunayen da ake sanya wa wasu jarirai sukan zame tamkar tambarin zolaya a kansu tare da musguna musu a lokacin yaranta lamarin da ke matsayin cin zarafi garesu a fagen rayuwa.

A gefe guda kuma batun rada kyakkyawar suna ga jariran da aka Haifa lamari ne da ya gudana a tsawon tarihin rayuwar Annabin Rahama Manzon Tsira Muhammadu dan Abdullahi da na iyalan gidansa tsarkaka {a.s}, inda suke radawa yaransu sunayen manyan mutane masu daraja da suka gabata tare da kwadaitar da mabiyansu kan yin hakan. Hakika wannan lamari yana matsayin girmamawa ne ga wadanda suka gabata kuma wani nau’in koyarwa ne ga yara da ke gagarumin tasiri a fagen tarbiyyarsu musamman tarbiyyar ruhi da na zamantakewa. Haka nan sanya wa yara sunaye masu kyau da kima lamari ne da ke kara habaka ruhin addini a tsakanin iyalan yara da ma al’ummar da suke rayuwa da su, kamar yadda watsuwar ruhin addini a tsakanin al’umma ke yin gagarumin tasiri a fagen kara tarbiyya da shiriyar yara a rayuwarsu ta nan gaba.

A bangare guda kuma idan har aka radawa mutum sunan manyan mutane masu daraja da girman matsayi misalin sunan Annabawa da Manzanni gami da wasiyyansu, a fili yake zaka ga mutum ba tare da nufi ko fadaka ba yana kokarin ganin ya gina rayuwarsa cikin tsarki da kamun kai irin tasu. Ya zo cikin ruwaya cewa; “A ranar kiyama za a zo da wasu mutane masu dauke da sunan Muhammadu, sai Allah Madaukaki ya ce; Shin ba ku ji kunyar gudanar da ayyukan laifuka ba duk da cewa kuna dauke da sunan masoyi na? To kasancewar kuna dauke da sunan masoyi na, Ni ina kunyan azabtar da ku”.

Yana daga cikin muhimman ladubbar tarbiyya gami da sunnah da ManzonTsira Annabin Rahama da iyalan gidansa tsarkaka {a.s} suka kiyaye tare da jaddada muhimmancinsa; gudanar da yanka gajaririn da aka Haifa musu. Tabbas ruwayoyi da dama sun zo kan muhimmancin gudanar da yanka ga jaririn da aka haifa, inda wasu daga cikin suke fayyace yankar tamkar wajibi ga mai hali da wadata, kuma har ya kasance jagororin shiriya na iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka {a.s} ba su amincewa da gabatar da sadaka a madadin gudanar da yanka ga jaririn da aka haifa.

Abdullahi bin Bukair yana cewa; Na kasance a wajen Imam Ja’afar Assadiq {a.s}, sai dan aikenAbdullahi dan Ali wato baffan Imam Sadiq {a.s} ya ce masa: Baffanka yana cewa; Na tafi neman dabbar da zan yanka a matsayin ragon suna amma ban samu ba, shin zan iya gabatar da kimar dabbar a matsayin sadaka? Sai Imam Sadiq {a.s} ya ce; “A’a, Hakika Allah ya ciyar da mutane abinci, kuma yana son a gabatar da dabba a matsayin hadaya”.

Hakika gudanar da yankar dabba a matsayin ragon suna, hakan yana da tasiri mai girma a fagen tarbiyyar jiki da na ruhin jaririn da aka yanka dabbar dominsa, saboda yankar tana daga cikin sunnonin addini musamman sunnar Annabi Ibrahim Khalil {a.s}, inda a maimakon yanka dansa Isma’il Allah Madaukaki ya fanshi ransa da dabba ta hanyar aiko da rago, inda hakan ya zame sunnah.

A karkashin koyarwar addinin Musulunci yanka ragon suna, yana nufin gabatar da hadayar dabba ce da nufin neman kusanci da yarda a wajen Allah Madaukaki da kuma neman kariya ga jaririn daga cututtuka da masifu a fagen rayuwarsa. Haka nan yanka ragon suna yana matsayin godiyan Allah kan ni’imar da ya yi ga mutum na azurta shi da yaro, saboda ya zo cikin ruwayoyi cewa; Yaro ni’ima ce daga cikin ni’imomin Allah Madaukaki. Sakamakon haka ya dace mutum a matsayin godiyar ni’imar da Allah ya yi masa ya gabatar da hadayar dabba, kuma mutum ya dauki matakin kautar da namar musamman ga mabukata saboda su kasance cikin farin ciki tare da taya shi murnar karuwar da ya samu.

Haka zalika nonon uwa yana daya daga cikin muhimman abubuwa masu girman tasiri a fagen tarbiyyar jiki da na ruhin jariri. Tabbas babu wani nau’in abinci da yafi amfani ga jariri irin nonon uwa. A lokacin da mahaifiya ke shayar da jaririnta nono, ba kawai tana gina masa jiki ba ne, a’a baya ga gina jiki tana kuma gadar masa da wani nau’in soyayya da jin kai da kuma tausayi. Bayan nan mahaifiya zata iya amfani da lokacin shayar da jaririnta nono wajen jiyar da shi karatun alkur’ani da ambaton Allah gami da addu’o’i domin ya tashi da sanin Allah da sauran abubuwa masu tsarki, sai jariri ya zame ya amfana da nonon mahaifiya da sauraron ayoyin alkur’ani mai girma, sakamakon haka sai jariri ya kasance ya tasirantu da abinci mai gina jiki da ruhi.

Har ila yau nonon mahaifiya baya ga gina jikin jariri da yake yi, kuma yana gagarumin tasiri a fagen karfafa ruhi da tunaninsa. Kan haka malaman tarbiyyar Musulunci suke cewa; Idan har yaro ya kasance yana sauraren karatun alkur’ani da addu’o’i, babu mamaki ya kai ga babban matakin tarbiyya a rayuwarsa.


Ra'ayi