Apr 27, 2016 16:27 UTC
  • Muhimmancin Shayar Da Nonon Uwa

A cikin shirinmu na yau zamu ci gaba da bayyana muhimmancin shayar da jariri nonon mahaifiyarsa ce, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa.

Masu saurare barkanku da warhaka, kuma barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na “Yara manyan gobe”. A shirinmu da ya gabata mun tabo batun muhimmancin nonon uwa ne da gagarumin tasirinsa a kan jaririnta musamman a fagen habaka lafiyarsa na jiki da na ruhi. Haka nan gudanar da karatun alkur’ani mai girma da ambaton Allah Madaukaki gami da addu’o’i a lokacin shayar da jariri. Kamar yadda nonon uwa ke da tasiri a fagen magance matsalar bullar tamowa ta hanyar kara lafiyar jikin jariri da gadar masa da lafiya da nutsuwa. A cikin shirinmu na yau zamu ci gaba da bayyana muhimmancin shayar da jariri nonon mahaifiyarsa ce, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa.

Hakika nonon uwa shi kadai zai iya rike jariri har zuwa watanni shida tare da gadar masa duk wasu matakan girman jiki da lafiya, don haka a tsawon wannan lokacin babu bukatar shayar da shi ko ciyar da shi wani nau’in abinci.

Ya zo cikin ruwaya cewa: Imam Ja’afar Sadiq {a.s} yana wasici ga matarsa cewa; Shayar da jariri nono daga dukkanin bakin nono biyu yana wadatar da jariri daga ruwa da abincin da yake bukata. Wato shayar da jariri daga bakin nono guda yana matsayin ruwan da yake bukata ne, sannan shayar da shi daga daya bakin nonon yana matsayin abincin da ke bukata.

Haka nan bincike na ilimi ya tabbatar da cewa; Ruwan nonon da ke fara fitowa mai ruwa-ruwa a lokacin da mahaifiya zata shayar da jaririnta, to wannan nonon yana matsayin ruwan da jariri ke bukata ne kuma yana kawar masa da kishin ruwa, sannan ruwan nonon da ke ci gaba da fitowa daga mahaifiya mai kauri, shi ne yake matsayin abincin da jariri ke bukata a rayuwarsa na wannan lokacin.

Haka nan farkon nonon da ke fitowa daga kirjin uwa bayan ta haihu mai launin yalo, wannan nonon yana dauke da wasu sinadarai masu amfani da kima kuma wannan ruwan nonon yana matsayin riga kafi ne ga jariri domin kare shi daga nau’o’in cututtuka, sakamakon haka mahaifa su tabbatar sun shayar da jariransu wannan ruwan nonon.

Har ila yau nonon uwa shi ne nau’in nonon da yafi duk wani nonon da za a shayar da jariri tsabta saboda nono ne da zai zuka kai tsaye daga jikin uwa, sabanin nonon da za a tatso daga dabba, ko nonon da ake sarrafawa daga kamfanoni inda a wani lokaci wannan nonon zai iya cin karo da wata kayar cuta kafin a kai ga shayar da jariri.

Hakika a kullum nonon uwa tsabtatacce ne kuma sabon nono da baya tsufa, sabanin sauran nonon da ake sarrafawa watakila akwai tsawon lokacin da ake diba masa domin yin amfani da shi, wato da zarar ya kai wannan wa’adi to nonon ya lalace kuma zai iya zama guba da zai cutar da lafiyar jariri.

Tabbas wasu kwararrun likitoci a fuskar kiwon lafiya da masana harkar shari’a suna da ra’ayin cewa; Nonon mahaifiya hakkin yaron da ta haifa ne, kuma babu wani mutum da ke musun cewa nonon uwa yana da tasiri a fagen samar da kwanciyar hankali da nutsuwa ga jarirai. A gefe guda kuma ‘yan jari hujja da wasu kungiyoyin da suke riya kare hakkin mata da suka yi fice a fagen shan jinin mata ta hanyar aikatar da su, suna yada farafagandar karya cewa; matakin da mata ke dauka na haihuwa tare da shayar da jariransu nono yana rusa musu rayuwa tare da ramar da su lamarin da ke kai ga haramta wa jarirai shan nonon uwa.

Hakika irin wadannan kungiyoyi suna kokarin ganin har yaran da suka tashi a yammacin turai tare da amfana daga nonon mahaifansu su girman cikin mummunan halin kadaici da firgita tamkar marassa uwa saboda rashin amfanuwa daga jin kan uwa da kusancinta ga yaranta, sakamakon shagaltar da ita da wasu ayyukan da zasu kawar da hankalinta daga rungumar ‘ya’yanta domin rainonsu. Haka nan mahangar irin wadannan kungiyoyi ta rashin jin kai da tausayi tana da bam mamaki a fuskar zamantakewar iyali. Wasu daga cikin irin wadannan kungiyoyi saboda tsabar rashin tausayi da jin kai ga yara; suna adawa tare da yin Allah wadai da duk wani tunanin daukar mace a matsayin mahaifiya da take dauke da dabi’ar tausayi da jin kai, sannan suna fassara hakan a matsayin zalunci ga mace da kokarin mai da ita saniyar ware.

Shulamith Firestore daya daga cikin masu tsaurin ra’ayin kare hakkokin mata a kan tubalin wuce gona da iri yana bayyana cewa; “Dole ne shafe batun daukar mace a matsayin uwa a shafin rayuwar dan –Adam”. A mahangar Shulamith yana ganin za a iya maye gurbin shayar da nonon uwa da bai wa jarirai madara a gora tare da kula da tarbiyyarsu a gidajen raino.

A gefe guda kuma mahangar addinin Musulunci yana daukar mace ce a matsayin uwa mai muhimmanci a fagen rayuwa, saboda kasancewar mace a matsayin uwa hakan baya nufin kakkabeta daga hakkokinta ko katangeta daga gudanar da ayyuka da hidima a fagen rayuwar zamantakewar jama’a, don haka nau’in halittar mace da dabi’arta wasu babbar dama ce gare ta da zai bata sukunin samar da yara lafiyayyu kuma nagari ga al’umma. Duk da cewa babu mai musun cewa tabbas a lokacin da mace take dauke da juna biyu da lokacin haihuwa da kuma lokacin shayar da jaririnta da kuma tsawon lokacin tarbiyyantar da shi tana fuskantar tarin matsaloli da wahalhalu, amma dabi’ar kasancewarta mahaifiya da kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da jaririn da ta haifa hakan zasu shafe mata dukkanin wahalhalu da matsalolin da ta fuskanta a tsawon wadancan lokuta tare da jin yarda da aminci a zuciyarta.

Tabbas matakin da wasu mata suke dauka a wannan zamani a sassa daban daban na duniya na nisanta daga yaransu sakamakon ayyukan da suke gudanarwa a wajen gida, a fili yake cewa babu wani abin da zai maye matsayin uwa tare da zaman madadinta, saboda duk wani wajen rainon yara bai zai taba maye gurbin uwa a fagen nuna jin kai, tausayi, rarrashi, nutsuwa da kwantar da hankalin yaro ba. Sakamakon haka addinin Musulunci ya jaddada matsayin uwa a fagen rainon danta domin gadar masa da nutsuwa, kwanciyar hankali, aminci da zaman lafiyan jiki da na ruhi. Don haka yaron da ya samu babban rabo a tsakanin al’umma shi ne wanda ya samu cikakken kula da raino daga mahaifansa musamman karkashin kulawar uwa.  


Ra'ayi