• Hashimi Rafsanjani: Dan Siyasa Mara Tamka:
                    (1)

Hashimi Rafsanjani: Dan Siyasa Mara Tamka: (1)

Labarin mutuwarsa ya jefa miliyoyin Iraniya da kuma masu kaunar juyin musulunci a wajen Iran cikin alhini. Domin kuwa Ayatullah Hashimi Rafsanjani shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci, ya kasance cikin na farko-farkon 'yan gwgawarmaya wadanda su ka kasance a tare da Imam Khumain   ( r.a). Dubun dubatar mutane ne su ka taru a bakin asibitin da aka kwantar da shi ana yi masa aiki bayan da ya samu matsalar zuciya.

Ba a  kuwa dauki lokaci mai tsawo ba aka sanar da rasuwarsa a asibitin shahidan Tajrish da ke kudancin birnin Tehran. Jagoran juyin musulunci Ayatullah Sayyid Khamnei ya fitar da bayani akan rasuwar ta Ayatulah Hashimi Rafsanjani inda ya ke juyayin rashin abokin gwagwarmayarsa da cewa:

"Rashin abokin gwagwarmaya kuma abokin tafiya da wanda tarihin tarayyarmu a aiki da abota ya kai shekaru 59 da su ka kasance cikin tsanani da wahala.!

 Wahalhalun da mu ka shiga tare a cikin wadannan shekarun suna da yawa, kuma abotarmu ta kasance cikin kyakkyawar niyya a wacce ta ci zango-zango daban-daban akan tafarkin da mu ka yi tarayya da shi, cikin tarbar aradu da ka.

Kaifin kwakwalwar da ya ke da ita, da kuma tsarkin niyyarsa mara tamka a tsawon wadannan shekarun, ya kasance wanda ake jingina da shi cikin nutsuwa da gaskatawa ga dukkanin wadanda su ka yi aiki da shi, musamman ma dai ni."

Jagoran juyin ya kuma jinjinawa Rafsanjani da cewa;

"Ya kasance abin koyi mara tamka, na zangon farko na 'yan gwagwarmayar da tsarin zalunci na sararuta, kuma yana cikin wadanda aka azabtar akan wannan godaben wanda ya ke cike da hatsari da kuma alfahari. Shekarun zaman kurkuku da dauriyar azabtarwa a hanun Savak, ( jami'an leken asirin Sha) da tsayin daka wajen fuskantar wannan, da aiki mai hatsari a lokacin yakin tsaron kasa mai tsari ( yaki da Iraki) da shugabanicn majalisar shawarar musulunci da majalisar kwararru, da waninsu, suna daga cikin shafuka masu haske na rayuwar wannan tsohon dan gwagwarmayar da ta kasance cike da fadi tashi.

Yanzu da aka yi rashin Hashimi Rafanjani, babu wani mutum da na sani wanda muka yi tarayya da shi akan abubuwa masu yawa na tsawon lokaci, mu ka kuma ga fadi tashi a cikin wannan lokaci na tarihi. "

A bisa kalandar Iran,marigayi Hashimi Rafsanjani wanda ya jagoranci majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci a Iran, ya rasu ne a ranar da aka kashe Amir Kabir shugaban gwamnatin Iran shekaru 165 da su ka gabata. Amir Kabir Kuwa ya kasance mai neman kawo sauyi a Iran a wancan lokacin. Ya rayu ne a loakcin gwamnatin Nasirud Din Sha wanda ya shiga tarihin Iran a matsayin mafi rashin makamar aiki a karkashin daular Qajar. Ya kuwa yi muliki ne na tsawon shekaru uku da rabi.

Ayyukan da Amir Kabir ya yi domin kawo sauyi da kuma samar da ci gaban Iran, ya jawo masa makiya a cikin gida da kuma waje. Gwamnatin Birtaniya na cikin wadanda su ka rika kitsa masa makirci domin ganin bayansa, a karshe sarkin ya daure shi sannan kuma ya sa aka kashe shi.

Sai dai duk da hakan, Sunan Amir Kabir ya shiga tarihin Iran ya kuma zama wanzajje.

Ayatullah Hashimi Rafsanjani yana ganin kima da daraja da matsayin Amir kabir. A zamanin gwgawarmaya da tsarin sarauta na Pahlawi, Ayatullah Hashimi Rafsanjani ya rubuta littafi akan Amir Kabir da gwagwarmayarsa ta kalubalantar 'yan mulkin mallaka.

                                                     ***

An haifi Hashimi Rafsanjani ne a shekarar 1935 miladiyya a kauyen Bahraman da ke karkashin garin Fafsanjan a gundumar Karman. Mahaifinsa ya kasance mai kiro da addini kuma manomi. Yana dan shekaru 14 ne ya tafi zuwa zuwa birnin Qum domin yin karatun addini. Bai kuwa dade da shiga fagen neman ilimi ba, ya kuma tsunduma a cikin fagen gwagwarmaya.

Bayan juyin mulkin da Birtaniya da kuma Amurka su ka yi a Iran a 1953 da su ka kifar da gwamantin Dr. Musaddaq, Akbar Hashimi Rafsanjani ya fara gwagwarmaya gadan-gadan. Kuma a wannan shekarar ne, ya hadu da Ayatullah Sayyid Ali Khamnei su ka yi sanayya da juna. Haka nan kuma da Imam Khumaini. A wancan lokacin Imam Khumaini bai kai ga zama marjanin da ake yi wa takalidi ba. Amma yana cikin malamai masu koyarwa a cikin cibiyar ilimin addinin musulunci ta Hauza.

 Sannu a hankali Hashimi Rafsanjani ya zama daya daga cikin almajiran Imam Khumaini.

Baya ga ci gaba da karatu da kuma gwagwarmaya, Hashimi Rafsanjani ya kasance mai taka rawa a fagen rubuce-rubuce a mujallar dalibai ta "Maktabu Tashayyui"

Bayan juyin mulkin 1953, Muhammad Ridah Pahlawi, ta samu cikakken goyon baya daga Amurka da Birtaniya. Kuma saboda gwamnatinsa ba ta da goyon bayan al'ummar kasar, sai ya dogara da 'yan mulkin mallaka domin su ba shi kariya. Don haka ya yi kokarin sauya dokokin cikin gida da yawa da kuma yin wasu ayyuka da ya kira farin juyin juya hali.

Sai dai a hakikanin gaskiya wadannan sauye-sauyen suna a matsayin wani yunkuri ne na shigo da al'adun turai  acikin Iran. Haka nan kuma bada dama ga Amurka da Birtyaniya domin su tatsi tattalin arikin Iran.

 

 

 

Jan 15, 2017 13:50 UTC
Ra'ayi