Sep 11, 2017 18:14 UTC

Kurdawa Da Yunkurin Ballewa.                              ( 1)

                 

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan fitowar ta shirin mu leka mu gani. Shiri ne wanda mu ka saba kawo mu ku batutuwan da suka shafi fuskoki daban-daban na rayuwa.

To ayau za mu far kawo mu ku shiri ne akan batun kuri'ar raba gardama da kurdawan Iraki su ke son yi dangane da ballewar yankin nasu da maida shi zama kasa mai cin gashin kanta.

Za mu dubi ne akan abubuwa daban-daban da za su iya faruwa idan hakan ta faru, haka nan kuma abubuwan da za su iya hana hakan faruwa.

Har ila yau za leka kundin tarihin kurdawan Irakin a cikin shekaru 97 da suka gabata.

Da fatan za a kasance a tare da mu domin a yi bangare na farko na shirin.

                            ****

Kurdawan Iraki Daga 1920 zuwa 1991

 

Tare da cewa a shekarar 1932 ne Birtaniya ta kawo karshen mulkin mallakarta a Iraki, amma samar da wannan kasar kamar yadda take a yanzu, ya fara ne tun a 1920. A hakikanin gaskiya a wancan lokacin ne da daular Usmaniyya ta rushe  'yan mulkin mallakar Birtaniya su ka shuka irin sabani da banbanci na kabilanci a cikin kasar.

Shugabannin kasar Iraki, sun yi kokarin rusa al'adu da duk wani abu da al'ummar Kurdawa suka kebanta da su, da kokarin damfara musu al'adun larabci. Wannan ya faru a tsakanin shekarar 1920 zuwa 1970. A wannan tsakanin ne kuma akidar larabci na Ba'asiyya ta kafu a Irakin wacce ita ce abinda ta sa       gaba kenan. Sai dai a daya gefen kurdawan sun rika yin bore da tawaye. Sun yi a cikin shekarar 1920, da 1930 da 1940 da 1960 da 1970 da 1980. Jagoran da ya fi yin fice a yunkurin na Kurdawa shi ne; Mulla Mustafa Barzani.

A cikin watan Maris na 1970 ne aka cimma yarjejeniyar a tsakanin gwmanatin Iraki da Mustafa Barzani akan bai wa yankin Kurdawa  kwarya-kwaryar gashin kai, da kuma maida harshen kurdawa a matsayin na biyu bayan larabci. Haka nan kuma shigar da Kurdawa a cikin gwmanati da mukaman soja, haka nan koyar da al'adun kurdawa.

Wannan yarjejeniyar iyakarta kan takarta amma a aikace ba ta sami wuri ba.

A wajajen 1970 ne jayayya da rikici akan al'adun da ya kamata kasa ta damfaru da su, ta kai koli. Jam'iyyar Ba'asiyya ta kai ga darewa kan karagar mulki a 1968 a Iraki. Siyasar da Saddam ya bulle da ita, ita ce ta mayar da Kurdawa su zama larabawa. Ya rika rushe garuruwansu da kuma dauke su daga garuruwansu na kaka da kakanni zuwa wasu yankuna.

A tsakanin 1975 zuwa 1991 ne Kurdawa suka rayu cikin tsanani mafi muni na tarihinsu. Sadam ya hana yin magana da harshen kurdawa a baina jama'a, ko cibiyoyin hukuma. An kuma hana Kurdawa rada sunayensu na gargajiya sai dai na larabci. Kurdawa sun bai wa waccan siyasar ta Sadam suna; "Ta Kashe harshe"

Kekashewar zuciyar Sadam akan Kurdawa, ta kai koli a cikin shekarar 1988. Ya bai wa dan kawunsa Ali Hassan Majid umarnin yin farmakin da ake bai wa sunan; ANfal" akan Kurdawan. Don haka ya yi amfani da makamai masu guba akan Kurdawan a cikin kauyukansu. Wannan ne ya sa aka sanya masa sunan: "Ali Mai Guba"

 Garin Halabjah na daga cikin garuruwan suka fuskanci mummunan harin na makamai masu guba.

Manufar gwamnatin Iraki shi ne rusa duk wani salo na gwagwarmayar Kurdawa da suke son ballewa domin kafa kasarsu. A karkashin waccan farmakin an rusa kauyuka da garuruwan Kurdawa 4000. Kuma fiye da mutane 180,000 ne aka kashe. Yayin da wasu dubun dubata su ka zama 'yan gudun hijira.

              Kurdawan Iraki Daga 1991 zuwa 2003.

Kudawa sun bude sabuwar rayuwa a farkon 1990,s. A shekarar 1991 ne suka yi wa gwamnatin Sadam bore, wanda kuma kwamitin tsaro na Majalisar  Dinkin Duniya  ya fitar da kuduri mai lamba 688 da ya goyi bayan Kurdawan. Kuma aka hana sojojin Irakin shiga yankunan arewacin kasar da Kurdawan suke. Wancan kudurin na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya sa a karon farko an yanke alaka a tsakanin yankin Kurdawa da gwamnatin Bagadaza.

Daga wancan lokacin ne kuwa, yankin na Kurdawa ya bude sabuwar rayuwa. An kafa majalisar yanki da kuma gwamnati. A cikin watan Mayu na 1992 a yankin na kurdawa ana kafa majalisa.

Sai dai an jingine aikin majalisar saboda yakin basasa da ya barke a tsakanin manyan jam'iyyun siyasa na kurdawa guda biyu daga 1994 zuwa 2002.

Sha'anin tafiyar da mulki a yankin Kurdawa yana a hannun Pira minista ne da kuma ministoci. Birnin Arbil ne cibiyar tafiyar da mulkin yankin Kurdawa.

Sai dai an kafa wata majalisar a garin Sulaimaniyya wacce manufarta kawo karshen yakin basasa a tsakanin jam'iyyun na kurdawa. Jam'iiyar farko ita ce ta Kursitan Democratic Party a karkashin Masud Barzani. Sai jam'iyyar Patriotic Union Of Kurdistan a karkashin Jalal Talabani.

A shekarar 1988, wato shekaru 4 bayan da jam'iyyun biyu suka kawo karshen yakin da su ke yi ta hanyar shiga tsakanin Amurka, an kulla sulhu wanda aka fi sani da sulhun Washington.

Yarjejeniyar ta kunshi kawo karshen yanki da kuma kafa majalisa da gwamnati ta hadin gwiwa a tsakaninsu. Don haka yanayin da yankin Kurdawa yake ciki a yanzu, ya samo asali daga waccan yarjejniya. An kafa majalisa a 2002 kuma yarjejeniyar ta 1998 ce ta share fagen yi wa yankin tsarin mulki na kashin kanshi.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tags

Ra'ayi