• Mahangar Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Dangane Da Take Hakkin Bil'adama A Iran:! ( 3)

Cutar Zika Da Alakarta Da Yakin Muggan Kwayoyi!

A cikin shirin da ya gabata mun yi alkawalin gabato muku da bayani akan bullar cutar nan ta Zika wacce ta ke haddasa nakasu na halitta a jikin jarirai. Cutar dai ta yi kama da zazzabin nan (Dengue) da sauran cutukan da aka sansu a yankin yammacin tekun Nilu.

An kuma bayyana cewa Sauro shi ne wanda ya ke dakon wannan cutar wanda daga kansa ta samo sunanta.

Iyaye mata masu juna biyu ne su ka fi saurin daukarta, sabod ahaka jariran da su ke haihuwa su ke zuwa da tawaya ta halitta, kamar karamin kai.

Kungiyar lafiya ta duniya ta byyana cewa; A cikin kasar Brazli kadai mutane miliyan 4 ne su ke fuskantar hatsarin kamuwa da wannan.

Kwayoyin cutar ta Zika suna yaduwa cikin sauri a duniya. Kawo ya zuwa yanzu dai babu wani magani wanda ya ke kashe ta. Ko kuma maganin rigakafinta.

Tambayar da masana su ke yi daga ina wannan cutar ta fito ko ya aka yi take yaduwa?

 

A baya dai an yi cuta irin wannan a nahiyar Afirka, amma dai a lokaci guda ba ta tsanani har haka ba.

 

Masana sun yi imani da cewa sani sauyi komai karancinsa da aka samu a cikinin kwaron da ya ke daukar ta. Kuma yau da gobe ta tabbatar da cewa abu ne mai yiyuwa ya zama da gangana akan yada wannna cutar.

 

Cibiyar nazari ta Rantis, ya fitar da wani bayani a baya da a ciki ta bayyana cutar da cewa yaki ne akan muhalli. Kuma abu ne mai yiyuwa Amurka yana da hannu a ciki. Cibiyar ta ci gaba da cewa:'

 

" Sauron da ya ke dauke da wannan cutar an sauya masa halitta ne a cikin wata gona ta Bill Gate."

 

Kuma ya watsu ne a cikin yankin Latin Amurka.

Rahoton ya ci gaba da cewa; Bil Gate, ya kafa wata gona a cikin watan Augusta na 2015 da kudin da su ka kai dalar Amurka miliyan 160.Ya saye ta ne daga jami'ar Oxford domin gudanar da nazarce-nazarce da bincike.

 

Wannan ra'ayi, yana da dalilai masu yawa da su ke tagaza masa da karfafa shi. Domin kuwa yana Magana ne akan yakin makamai masu guba. A cikin yaki irin wannan kuma ana amfani da kwayoyin cuta kowadanne iri a matsayin makami. Kuma komawa baya da yin waiwaye zai yaye kallabin yadda Amurka ta ke a matsayin ta gaba wajen kera da samar da wannan nau'oin makaman yaki. Ta dade tana kera makamai masu guba da cutuka.

 

Kamfanonin Amurka masu yin magunguna sun sha yin gwajin wasu magungunan na cuta akan mutane a nahiyoyin Afirka da kuma Asiya da kuma yankin Latin. 'Yan salin Amurka, da ake kira Indiyawan daji, suna daga cikin wadannan aka rika gwaji da su. Da dama daga cikinsu sun mutu saboda cutuka

 

Sojojin Ingila ma sun taba amfani da cutar kyanda a matsayin makamin yaki. Sun yi amfani da kwayoyin cutar akan kabilar Pontiac ta Indiyawan daji a 1763. A wannan shekarar kuma 'yan ci-ranin da su ka zauni Amurka sun yi amfani da wadannan kwayoyin cutar na kyanda akan 'yan kasa na asali.

Kuma a lokacin yakin duniya na biyu, Ingila da Amurka sun shirya kai wa wasu garuruwan Jamus hari da kwayoyin cuta na Bakon dauro. A shekarar 1952 Amurkan ta yi amfani da makamai masu dauke da guba da cuta akan mutanen korea.

 

Shafin labaru na Faransacni na a'Tranfor' ya gudanar da bincike mai zurfi akan wannan batun.

 

Hatta a lokacin yakin tekun Pasha ma Sojojin Amurka 150,000 sun cutu daga makaman da aka yi da su, masu dauke da cutuka, Kuma wasu da dama daga cikin sojojin sun mutu ne sanadin hakan.

 

A karkashin nazari da bincike na aikin likitanci, an bude wannan irin yaki akan bil'adama. A kan tuddan Mireland na Amurka da akwai wata cibiyar nazari da bincike ta sojan Amurka wacce ta taka rawa a lokacin yakin duniya da kuma yakin cacar baki. Wuri ne na gudanar da bincike akan muggan cutuka da nau'oi daban nasu.

 

***

Kamfanonin kera magunguna sun yi gwaji akan mutane a kasashe daban-daban. Dr. Cornailson ya rika dura wa mutane cutar sankara cikin sani a 1931. Shi kuwa yana daga cikin wadanda su ka kafa cibiyar nan na bincike ta Rockfellas.

A kasar Guatemala ma Amurkan ta yi gwajin wasu cutukan akan mutanenta 1932. Haka nan kasashe da daman a yankin latin sun zama zakaran gwajin dafin irin wadannan kamfanonin na Amurka a shekarun baya.

 

Kamfanin Pfizer ya yi gwaji akan kananan yara a kano a 1996. Daruruwan yara ne dai su ka kamu da cutuka da su ka zama sanadin nakasa su, baya ga wadanda su ka mutu.

 

 

 

 

Jun 25, 2016 14:09 UTC
Ra'ayi