Nov 21, 2016 11:45 UTC
  • Gwamnatin Maroko Ta Jaddada Aniyarta Ta Murkushe Kungiyoyin 'Yan Ta'adda A Kasar

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Maroko ta jaddada aniyarta ta murkushe kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin kasar.

A bayanin da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Maroko ta fitar a yau Litinin yana dauke da cewa: Jami'an tsaron kasar suna cikin shirin ko-ta kwana domin daukan matakin murkushe dukkanin kungiyoyin 'yan ta'adda da suke ci gaba da zama barazana ga kasar musamman kungiyoyin Da'ish da na Jubhatun-Nusrah.

Bayanin ya kara da cewa: Kungiyoyin 'yan ta'addan suna shirye-shiryen kaddamar da hre-haren wuce gona da iri kan ma'aikatun gwamnatin kasar da na cibiyoyi masu zaman kansu, amma jami'an tsaron Maroko suna cikin shirin kalubalantar wannan bakar aniya ta 'yan ta'addan.

Majiyar tsaron Maroko dai ta bayyana cewa: Tun daga shekara ta 2002 zuwa yanzu ta samu nasarar murkushe cibiyoyin 'yan ta'adda 152 a sassa daban daban na kasar, kuma 31 daga cikinsu suna da alaka ta kai tsaye ne da kungiyar ta'addanci ta Da'ish.  

 

Tags