Apr 29, 2017 17:02 UTC
  • Bincike Yana Nuni Da Cewa Tashe-Tashen Hankula A Sudan Suna Janyo Matsalar Kwakwalwa

Wani sabon bincike a kasar Sudan yana nuni da cewa: Tsawon lokacin da aka dauka ana gudanar da yaki a yankin Kudancin Darfur da ke kasar Sudan ya janyo bullar matsalar kwakwalwa a tsakanin al'ummun yankin.

A bayanin da wata cibiyar bincike a kasar Sudan ta fitar dangane da binciken lafiyar jama'a da aka gudanar a yankin da ke kudancin Darfur da aka dauki tsawon lokaci ana dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin Sudan da 'yan tawayen kasar, binciken yana nuni da cewa; Mutane Akalla 423 ne suke fama da matsalar kwakwalwa ko tabin hankali musamman irin mutanen da yaki ya rusa musu tsarin rayuwar iyali da na zamantakewa gami da na tattalin arziki.

Wani masanin halin zamantakewar al'umma a kasar ta Sudan mai suna Muhammad Abbakar Isah yana cewa: Yaki a yankin Darfur baki daya ya haifar da matsalolin tabin hankali da firgita a tsakanin al'ummun yankin, kuma rashin cibiyar lafiya mai kula da matsalar kwakwalwa a yankin ya kara janyo yawaitar matsalolin tabin hankalin.

Tun a shekara ta 2003 ne yakin basasa ya kunno kai a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan sakamakon nuna halin ko-in kula da mahukuntan kasar suka yi kan matsalolin rayuwar al'ummar yankin lamarin da kai ga hasarar rayukan mutane fiye da 300,000 tare da tilastawa wasu fiye da miliyan biyu barin muhallinsu.

Tags