Jun 28, 2017 19:00 UTC
  • An yi Gargadi Akan Sake Bullar Wani Sabon Yaki A Gabacin Kasar Congo

Jami'an tafiyar da mulki a gundumar Kivo ta Arewa, sun gargadi sojojin kasar akan yiyuwar tsananta hare-haren 'yan tawaye da ke yankin

Jami'an tafiyar da mulki a gundumar Kivo ta Arewa, sun gargadi sojojin kasar akan yiyuwar tsananta hare-haren 'yan tawaye da ke yankin.

Kamfanin dillancin labarun AFP ya ambato Kantoman gundumar ta Kivo ta Arewa, 1.Julien Paluku yana cewa; Wajibi ne ga sojojin hadin gwiwa a yankin su ja daga domin fuskantar sabbin hare-haren a yankin.

Paluku ya yi wannan gargadin ne kwanaki biyu bayan da masu dauke da makamai a yankin Kasindi su ka kai hari akan iyaka tare da kashe sojojin kasar Uganda biyu.

Gabacin kasar Demokradiyyar Congo dai wata tunga ce ta kungiyoyin yan tawaye na cikin gida da kuma kasashen makwabta.

Tags