Mar 15, 2018 07:12 UTC

Gwamnatin Najeriya ta bayyana shirinta na ceto 'yan matan sakanderen Dapchi da mayakan boko haram suka yi awan gaba da su cikin watan da ya gabata.

Cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar Najeriya ta fitar, ta ce Shugaba Buhari a gwamace a ceto 'yan matan sakanderen Dapchi  da mayakan boko haram suka sace ta hanyar Lumana, a kuma  mayar da su wajen iyayensu cikin koshin lafiya, domin haka gwamnati ta bayyana shirinta na tattaunwa da 'yan boko haram din.

A ranar 19 ga watan Favrayun da ya gabata ce, mayakan Boko haram suka sumame a makarantar kwana ta sakanderen Dapchi dake jahar Yobe a shiyar arewa maso gabashin Najeriya, tare da sace 'yan mata 111,kuma har yanzu ba a ji duriyarsu ba.

Sace 'yan matan na Dapchi, wanda ya zo shekara hudu bayan sace 'yan matan Chibok, ya tayar da hankalin mazauna garin da ma jihar baki daya,kuma ya faru ne a daidai lokacin da gwamnati ke cewa ta karya lagon mayakan na Boko Haram.

Domin kwantar da hankulan iyayen 'yan matan da aka sace, a safiyar jiya Laraba, Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci garin Dapchi da ke jihar Yobe , inda aka sace 'yan matan sakandare fiye da 100 a watan da ya gabata, shugaban ya gana da iyayen yaran da aka sace a makarantar sakandaren, inda a nan ne aka sace 'yan matan.

A yayin ganawarsa da iyayen 'yan matan, Shugaba Buhari ya tabbatar musu da cewa gwamnati za ta yi iya nata kokari domin ganin ta ceto 'yan matan, kuma ya ce ba ya so a yi amfani da karfin tuwo domin kada a jefa rayukan yaran cikin hadari, a don haka a shirye yake ya tattauna da wadanda suka sace su.

A baya dai gwamnatinsa ta yi musayar mayakan Boko Haram da wasu daga cikin 'yan matan Chibok.

Yanzu haka dai gwamnatin Muhamadu Buhari na shan suka kan yadda ta tunkari sace 'yan makarantar, wanda aka hora alhakinsa kan kungiyar Boko Haram.kafin isar shugaba Buhari a makarantar ta Dapchi, iyayen yaran da aka sace sun yi dafifi a makarantar da aka sace 'ya'yan nasu inda suke jiran isar Shugaba Buharin don ganawa da su.wasu daga iyeyen sun bayyana cewa muna  jira ne shugaban ya zo ya gamsar da mutanen gari kan kokarin da gwamnati ke yi na ceto 'ya'yansu da kuma matakan da za a dauka don hana sake afkuwar irin hakan, daya daga cikin iyayen da aka tafi da 'yayanta guda biyu ta ce ta yi mamakin yawan jami'an tsaron da suka rako shugaban,shin ina sojojin suka shiga a lokacin da aka sace 'yayansu, wani kuma daga cikin ya bayyana shakunsa kan matakai da kuma kalaman shugaban kasar, inda ya ce  babu tabbas ga kalaman shugaban.

Yanzu dai abin jira a gani shine, wani mataki ne gwamnati za ta dauka na ganin an ceto wadannan 'yan mata? yaushe gwamnati za ta tattauna da kungiyar Boko Haram din? kuma yaushe za a sako 'yan matan suka koma wurin iyayensu kamar yadda ko wani dan Najeriya ke fata?wani mataki gwamnati za ta dauka na ganin irin wannan lamari bai faru ba a nan gaba?

Tags