Apr 20, 2018 18:55 UTC
  • An Cafke Wasu 'Yan Ta'addan Takfiriyyah 4 A Kasar Aljeriya

Ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya ta sanar da kame wasu 'yan ta'addan takfiriyya hudu da suka hada da wani gawuraccen kwamanda daga cikinsu.

Kamfanin dillancin labaran Xinhua ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da ma'aikatar tsaron kasar ta Aljeriya ta fitar a yau, ta sanar da kame Ilyas Abu Ayyub, wani babban kwanadan 'yan ta'addan takfiriyyah a yankin kudancin kasar, wanda ya shahara da ayyukan ta'addan a kasashen yankin magrib.

Haka nan kuma a wani farmaki da dakarun na Aljeriya suka kaddamar a yankunan arewa masu gabashin kasar, sun samu nasarar cafke wasu uku daga cikin 'yan ta'addan da ake nema, tare da samun tarin makamai da ababe masu fashewa tare da su.

kasar Aljeriya dai a halin yanzu tana fuskantar karuwar barazanar ta'addanci, musamman ma tun bayan da 'yan ta'adda suka fara tserewa daga kasashen Syria da Iraki suna komawa kasashensu na asali, sakamakon kashin da suke sha  ahannun dakarun kasashen na Iraki da Syria.

 

 

Tags