May 08, 2018 07:51 UTC
  • Majalisar Dokokin Najeriya Za Ta Amince Da Kasafin Kudade Na 2018

Shugaban majalisar dattijan Najeriya Abubakar Bukola Saraki da kuma shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara, sun sanar da cewa majalisun biyu za su amince da kasafin kundin na shekara ta 2018.

Shugabannin majalisun biyu sun sanar da hakan ne jim kadan bayan wata ganawa da sukayi da shugaba Buhari a fadar Aso Rock da ke Abuja, inda suka tabbatar da cewa a cikin wannan mako suke ran duba batun a majalisa, kuma akwai yiwuwar mako mai zuwa a maince da kasafin.

Tun bayan da bangaren zartarwa ya mika kasafin kudin kimanin watanni shida da suka gabata, 'yan majalisun suka ki amincewa da shi, inda ake ganin a halin yanzu an samu fahimtar juna tsakanin bangaren zartarwa da kuma majalisa a kan batun.

Tags