May 28, 2018 19:21 UTC
  • An Sake Kama Wani Jigo A Cikin Kungiyar Ikhwanul Muslimin Ta Kasar Masar

Babban mai gabatar da kara a kasar masar ya bada sanarwan sake kama daya daga cikin jagororin kungiyar yan uwa musulmi a yau litini don amsa tambayoyi.

Kamfanin dillancin labaran Aljazeera ya nakalto babban mai gabatar da kara na kasar ya masar yana fadara haka a safiyar yau litini, ya kuma kara da cewa tuni kotu ta bada umurnin a tsare Abdul-Mun'im Abulfutuh a gidan kaso na tsawon kwanaki 15 .

Abul Futuh dai shi ne shugaban Jam'iyyar "Misrul Qawi" kuma a farkon shekara ta 2018 ma an taba tsare shi bayan ya soki shugaban kasa Abdul Fatah Sisi kan yadda yake tafiyar da kasar.

Tun bayan kifar da gwamnatin Muhammad Mursi a shekara ta 2013 wanda sojoji suka yi, gwamnatin kasar Masar ta haramta kungiyar Ikhwanul Muslimin ta kuma sanyata cikin jerin kungiyoyin yan ta'adda.

Babban mai gabatar da kara na kasar ta Masar bai bayyana dalilin tsare Abulfutuh ba.

Tags