Jun 03, 2018 19:04 UTC
  • Jami'an Tsaron Kasar Aljeriya Sun Halaka 'Yan Ta'adda 24 A Cikin Wata Guda Kacal

Ma'aikatar tsaron Aljeriya ta sanar da cewa: A cikin wata guda kacal jami'an tsaron kasar sun yi nasarar kashe 'yan ta'adda 24 a sassa daban daban na kasar.

A sanarwar da ma'aikatar tsaron Aljeriya ta fitar ta bayyana cewa: A samamen  da jami'an tsaron kasar suka gudanar a sassa daban daban na kasar Aljeriya a cikin watan Mayun da ya gabata sun yi nasarar halaka 'yan ta'adda 24 ciki har da manyan kwamandojin kungiyar ta'addanci ta Al-Qa'ida a yankin arewacin Afrika tare da kame wasu 9 na daban.

Sanarwar ta kara da cewa: Gungun 'yan ta'adda ta mutane 17 ne suka mika kansu ga jami'an tsaron kasar a cikin watan na Mayu da ya gabata, kamar yadda jami'an tsaron na Aljeriya suka samu nasarar rusa maboyan 'yan ta'adda 108 tare da kwasar ganimar makamai a sassa daban daban na kasar. 

 

Tags