Jun 24, 2018 12:47 UTC
  • Burundi: An Kama Wani Jami'in Gwamnati Bisa Zargin Cin Hanci Da Rashawa

Gwamnatin Burundi ta sanar da kame jami'in gwamnatin a tare da wasu faransawa hudu bisa tuhumar almundahana ta kudade.

Kamfanin dillancin labarun Faransa ne ya nakalto majiyar tsaron kasar Burundi na cewa; Jami'in da aka kama, yana da hannu a cikin laifukan damfara da amfani da mukami ta hanyar da ba ta dace ba.

Sauran mutanen 'yan kasar Faransa an kama su ne a lokacin da suke kokarin ficewa daga kasar a filin saukar jiragen sama na Bujunbiri.

Jami'in da aka kama ya taba rike mukamin mai ba da shawara ga shugaban kasa sannan kuma ya rike mukamai na shugabancin kamfanoni daban-daban.

Tags