Jun 30, 2018 11:06 UTC
  • Moroko: An Kama Masu Zanga-zanga Da Dama

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakalto cewa; An kame mutane da dama masu Zanga-zanga a kauyen Bokidh da ke kusa da birnin al-Hsaimah bayan taho mu gama da jami'an tsaro.

Mazu Zanga-zangar dai suna nuna kin amincewarsu ne da hukuncin da wata kotu ta yanke akan jagoran yunkurin da aka fi sani da na mazauna karkara, Nasir alzazafi na zaman kurkuku tsawon shekaru 20.

A yayin taho mu gama din, yan sanda 10 sun jikkata, yayin da aka kame mutane da dama.

Tun a 2016 ne dai mazauna garin al-Husaimah suka fara Zanga-zanga domin nuna kin amincewa da kisan da jami'an tsaro su ka yi wa wani masunci. Tun daga wancan lokacin ne dai aka samar da wani yunkuri da ake kira na mazauna karkara, da suke nuna kin yardar da tabarbarewar harkokin tattalin arziki.

 

Tags