Jul 05, 2018 06:45 UTC
  • Aljeriya:An Hallaka 'Yan Ta'adda 20 Cikin Watani 6

Dakarun tsaron Aljeriya sun hallaka 'yan ta'adda 20 a cikin watani 6

Kamfanin dilancin labaran Irna ya nakalto ma'aikatar tsaron Aljeriya na cewa dakarun tsaron kasar sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda 20 da kuma cabke wasu 18 na daban a cikin watani shidan da suka gabata, sannan kuma wasu 66 na daban sun mika kawunansu ga jami'an tsaro.

Sanarwar da ma'aikatar tsaron Aljeriyan ta fitar ta kara da cewa cikin watani shidan farko na wannan shekara da muke ciki, dakarun tsaron kasar sun samu nasarar ruwa maboyar 'yan ta'adda 311 tare da kuma da wasu ma'aikatun kera makamai guda biyu a kasar.

Kasar Aljeriya na fama da matsalar safarar makamai da 'yan ta'adda, sanadiyar makwabtaka da kasashe kamar Libiya, Mali da suke fama da matsalar tsaro.

Baya ga tsaron iyaka, dakarun tsaron Aljeriyan sun samar da wuraren bincike da dama a cikin burane domin kalubalantar duk wani yunkurin ta'addanci a cikin kasar.

Tags