Jul 19, 2018 12:22 UTC
  • A Najeriya An Kama 'Yan Boko Haram Fiye Da 20

Majiyar 'yan sandan Najeriya ta sanar da kame mutane 22 'yan kungiyar Boko Haram wadanda suke shirya kai hare-haren kunar bakin wake.

Majiyar ta ci gaba da cewa mutanen da aka kama sun tsara da shirya kai hare-haren kunar bakin waje fiye da 50, haka nan kuma wadanda suka kitsa sace 'yan matan chibok shekaru 4 da su ka gabata.

A cikin watan Aprilu na 2014 ne 'yan kungiyar ta Boko Haram suka sace 'yan mata 275 daga makarantar kwana da take garin Chibok a jahar Borno. Har ya zuwa yanzu da kawai wasu daga cikin 'yan matan da ba dawo da su ba.

Tun a 2009 ne kungiyar Boko haram ta fara kai hare-haren ta'addanci a Najeriya wanda kawo ya zuwa yanzu ta kashe mutane fiye da 20,000.

 

Tags