Jul 23, 2018 07:12 UTC
  • Boko Haram Ta kashe Mutum 18 A Chadi

Wasu mayaka da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kashe mutane 18 da kuma yin awan gaba da mata 10, a lardin Dabua na Chadi dake yankin tafkin Chadi.

Lamarin dai ya auku ne a cikin daren ranar Alhamis da ta gabata, kamar yadda wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin dillancin labaren AFP.

Wannan dai na zuwa ne bayan sanarwar da rundinar sojin Nijar, ta fitar na cewa ta hallaka 'yan ta'adda goma, bayan da ta murkushi wani harin Boko haram kan wani sansaninta dake kudu maso gabashin kasar a cikin daren ranar Alhamis da ta gabata. 

Marabin Chadi ta fuskanci harin Boko Haram tun wani da ya yi sanadin mutuwar jami'an tsaronta 6 a watan Mayu na shekara 2018, a lardin Gabalami a kusa da Kinassarom a yankin tafkin Chadi.

Tags