Jul 27, 2018 04:42 UTC
  • Najeriya : Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Fi Na Boko Haram Muni, Inji ICG

Kungiyar International Crisis Group, dake nazari kan rikice-rikice a duniya, ta fitar da wani rahoto kan rikicin kabilanci a Najeriya wanda ke cewa, rikicin manoma da makiyaya a tsakiyar Najeriyar, ya fi na kungiyar Boko Haram muni.

A rahoton data fitar kungiyar ta ICG, ta ce rikicin na tsakanin manoma da makiyaya ya yi ajalin mutane sau shida idan aka kwatanta shi dana Boko haram a farkon wannan shekara.

Rahoton ya ce rikicin na manoma da makiyaya ya hadassa hasara rayukan mutane sama da 1,500 tun daga shekara 2017.

A watan Yuni da ya gabata rikici makamancin hakan, ya yi ajalin mutum sama da 200 a wasu kauyukan 11 dake yankin Barikin Ladi a jihar Filato.

Wanda rahoton ya ce sojoji da jami'an 'yan sanda sun kasa tabaka komai don tabbatar da tsaro da kuma gurfanar da wadanda keda hannu a rikicin, wanda ya kai ga mutanen yankin suka kai ga daukar matakan kare kansu.

Kungiyar ta International Crisis Group, ta bukaci mahukuntan Najeriyar akan su dauki duk matakan da suka dace na kawo karshen wannan rikici, musamman a daidai wannan lokaci da kasar ke fuskantar manyan zabukanta.

Rahoton ya ce rikicin na tsakanin manoma da makiyaya yana da nasaba da kabilanci da kuma addini, inda mafiya yawan makiyaya Fulani musulmai ne, a yayin da manoman mafiya rinjayensu Kristoci ne.

Tags