Aug 08, 2018 18:48 UTC
  • Jami'an Tsaron Zimbabwe Sun kame Daya Daga Cikin Jiga-Jigan 'Yan Adawar Kasar

Jami'an tsaron Zimbabwe sun kame daya daga cikin jiga-jigan 'yan adawar kasar a lokacin da yake kokarin tsallaka kan iyakar Zimbabwe domin gudu zuwa kasar Zambia.

Majiyar tsaron Zimbabwe ta sanar da cewa: Jami'an tsaron  kasar sun kame Tendai Biti daya daga cikin jiga-jigan gamayyar jam'iyyun adawar kasar da suka mara baya ga babbar jam'iyyar adawar Zimbabwe ta MDC da tasha kaye a zaben shugabancin kasar a lokacin da yake kokarin tsallaka kan iyakar kasar zuwa kasar Zambia.

Jami'an tsaron Zimbabwe sun tasa keyar Tendai Biti zuwa birnin Harare domin fuskantar tambayoyi kan zarginsa da hannu a tunzura jama'a domin gudanar da tarzoma bayan fitar da sakamakon zaben 'yan Majalisun Dokokin Kasar da na shugaban kasa lamarin da ya janyo hasarar rayukan mutane akalla shida tare da barnata dukiyoyi na miliyoyin kudade.

Tendai Biti dai shahararen dan siyasa ne a Zimbabwe kuma ya rike ministan kudin kasar a shekara ta 2009 zuwa 2013 a karkashin gwamnatin hadin kan kasa, kuma yana daga cikin magoya bayan Nelson Chamisa da ya sha kaye a zaben ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata. Wata majiya daga lauyar Tendai Biti ta bayyana cewa: An bada belinsa bayan amsa tambayoyi daga jami'an tsaron kasar.    

Tags