Aug 11, 2018 19:20 UTC
  • Kwamitin Tsaron MDD Ya Yi Allawadai Da Kai Hari Kan Dakarun UN A Afirka Ta Tsakiya

Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya yi Allawadai da wani farmaki da aka kaddamar kan dakarun majalisar a jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya fitar kan rikicin da jamhuriyar Afrika ta tsakiya take fama da shi, ya bayyana kai hari a kan dakarun kiyaye sulhu na kasa da kasa da cewa ba abu ne da za a lamunce da shi.

Kwamitin tsaron ya kirayi masu dauke da makamai a kasar da su ajiye makamansu, su rungumi sulhu da zaman lafiya da junansu.

Baya ga kungiyoyin 'yan bindiga masu fada saboda dalilai na siyasa da kabilanci, akwai kungiyoyin 'yan bindiga da dama da suke yaki da juna saboda hakar ma'adanai.

 

Tags