Aug 13, 2018 12:46 UTC
  • Masar: An Kama Wadanda Ake Zargi Da Shirya Kai Harin Kunar Bakin Wake

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar ta sanar da kame wasu mutane da suka shirya kai wa wata majami'a hari a arewacin birnin alkahira

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Masar ta ce mutumin da ya  kai harin  kunar bakin waken sunansa Umar Muammad Ahmada Mustafa, wanda haifaffen birnin alkahira ne.

A yayin harin babu wanda ya rasa ransa ko jikkata idan ba maharin ba.

Kawo ya zuwa yanzu babu wata kungiya wacce ta dauki nauyin kai harin. Da akwai kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin Sinan da ke kan iyaka da Palasdinu, wadanda su ke kai irin wannan harin na kunar bakin wake a Masar.

A baya, majamiun kasar da dama sun fuskanci kai hare-haren ta'addanci wanda kungiyar Da'esh take daukar alhaki

 

Tags