Aug 15, 2018 19:06 UTC
  • Yansanda A Najiriya Sun Gurfanar Da Danjarida Mai Aiki Wa Jaridar Premium Times A Gaban Kotu.

A yau laraba ce hukumar yansanda a Nigeria ta gurfanar da Samuel Ogundipe dan jarida mai aikiwa jaridar Premiumtimes ta kasar a gaban wata kutu a Abuja.

Jarudar ta Premiumtimes ta bayyana cewa yansanda sun kai Mr Ogundipe a gaban alkali a kotun Kubwa inda suka 

gabatar da kara tare da zarginsa da sace takardun yansanda na sirri da kuma shiga inda bai da izinin shiga.

Alkalin bayan sauraron karar ya bada umurnin a ci gaba da tsare shi na kwanaki 5 wato har zuwa 20 ga watan Augusta. 

Jaridar ta kara da cewa a gurfanar da shi a matsayin yan jarida, sun kuma zarge shi a bisa doka ta 352, 288 da kuma 319 na Penal Code.

Kafin a wuce da shi gidan yari Mr Ogundipe ya sami magana da Editan jaridar ta Premuim times inda ya bayyana masa halin da yake ciki.

An kam Mr Ogundipe bayan ya bada rahoto kan yadda jami'an tsaro na DSS suka yiwa majalisar dokokin Najeriya kawanya a cikin yan kwanakin da suka gabat.

 

Tags