Aug 20, 2018 06:43 UTC
  • An Tsananta Hare-Hare Kan Ma'aikatan Kungiyoyin Bada Agaji A Kasar Afrika Ta Tsakiya

Ofishin wakilin hukumar bada agaji ta majalisar dinkin duniya a birnin Bangi na kasar Afrika ta tsakiya ya bayyana cewa jami'an bada agaji na hukumar da sauran kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa suna fama da hare hare da kuma sata a wurare da dama a kasar.

Tashar radio ta "Radio Faransa na kasa da kasa" ta nakalto Najat Rishdy shugaban ofishin hukumar bada agaji na majalisar dinkin duniya a birnin Bangi babban birnin Afrika ta Tsakiya tana bayyana haka a jiya 19 ga watan Augustan wato ranar da aka ware don girmama kungiyoyin bada agaji a duniya. 

Rushdi ta ce daga farkon wannan shekara ta 2018 ya zuwa yanzu an kaiwa jami'an bada agaji 205 hare hare, sannan 103 daga cikinsu na satar kayakin aikinsu wadanda suka hada da abinci da sauransu. A wani labarin shugaban hukumar bada agaji na kasar Afrika ta Tsakiya ya bada sanarwan kissan jami'an bada agaji 6 a cikin wannan shekara da muke ciki a kasar. 

Tags