Aug 23, 2018 19:00 UTC
  • Jami'an Tsaro A Kasar Masar Sun Kama Shugaban Wata Jam'iyyar Adawa Na Kasar

Wasu kafafen yada labarai sun bada labarin cewa an kama wani dan adawa da gwamnatin kasar saboda bada shawarar a gudanar da zaben raba gardama a kan shugabancin shugaba Abdulfattah Assisi.

Shafin yanar gizo na tashar talabijin ta Aljazira ta nakalto dan rahoton tashar Khalid Ali yana fadar cewa jami'an tsaron kasar sun kama Masoom Marzuk wani dan adawa da gwamnatin Abdul fattah assisi wanda ke zama a kudancin Alkahira babban birnin kasar a yau Alhamis kuma har yanzun ba'a san ina aka je da shi ba.

A farkon watan Augusta da muke ciki ne dai Masum marzuk ya bukaci a gudanar da zaben raba gardama don ci gaba da shugabancin shugaba Abadul fattah Assisi a kasar. Ya kuma kara da cewa idan gwamnatin kasar ta ki amincewa da zaben raba gardama to kuwa mutane su fito zanga zangar neman murabus din shugaban daga kan kujerar shugabancin kasar a ranar 31 ga watan Augusta. 

Marzuk dai tsohon jami'an diblomasiyyar kasar ne sannan ya taba rike mukamin mataimakin ministan harkokin wajen kasar. 

Tags