Aug 24, 2018 06:22 UTC
  • Jami'an Tsaron Masar Sun Yi Awungaba Da Wani Fitaccen Dan Adawa A Kasar

Jami'an tsaron Masar sun kame wani fitaccen dan adawa a kasar da ya nemi gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a kan makomar shugaban kasar Abdul-Fatah Al-Sisi na ya ci gaba da mulki ko kuma ya yi murabus.

Shafin watsa labarai na Aljazeera ya habarta cewa: Jami'an tsaron Masar sun kai samame yankin yammacin birnin Alkahira fadar mulkin kasar a jiya Alhamis, inda suka yi awungaba da Ma'asum Marzouk shahararren dan adawar siyasa a kasar.

Tun a farkon wannan wata na Agusta ne Ma'asum Marzouk ya gabatar da bukatar gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a a kasar Masar domin tantance makomar shugabancin Abdul-Fatah Al-Sisi, kuma matukar mahukuntan kasar suka ki amincewa da wannan bukata tashi, to yana kira ga al'ummar Masar su fito zanga-zangar lumana a ranar 31 ga wannan wata na Agusta domin jaddada rashin amincewarsu da jagorancin Abdul-Fatah Al-Sisi.

Ma'asum Marzouk dai tsohon jami'in diflomasiya ne a Masar, kuma ya taba rike mukamin mataimakin ministan harkokin wajen kasar, kamar yadda ya yi fice a fagen nuna adawa da matakin da shugaban kasar Abdul-Fatah Al-Sisi ya dauka na mika tsibiran kasar Tiran da Sanafir ga kasar Saudiyya.    

Tags