Aug 24, 2018 19:01 UTC
  • Jami'an Tsaro A Kasar Masar Sun Ci Gaba Da Kama Fitattun Masu Adawa Da Gwamnatin Kasar

Jami'an Tsaro a kasar Masar sun kama wasu karin fitattun yan adawa da gwamnatin kasar, inda a jiya Alhamis suka kama Raed Salama mamba a jam'iyya mai adawa ta "Al-Karamah" da kuma Yahya Kazaz wanda shi ma fitaccen mai adawa da gwamnatin Abdulfattah Assisi ne.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayyana cewa kafin haka ma jami'an tsaron kasar ta Masar sun kama Masuom Marzuk wani tsohon jami'in diblomasiyyar kasar wanda kuma ya taba rike mukamin mataimakin ministan harkokin wajen kasar. Labarin ya kara da cewa ya zuwa yanzun babu wata tuhuma da ake wa mutanen ukku tun bayan kamasu.

Kafin a kama shi, Masoim Marzuk ya bukaci mutanen kasar Masar su nemi gwamnatin Abdulfatah Assisi ta gudanar da zaben raba gardama don fayyece makomarsa kan shugabancin kasar. 

Tun bayan juyin mulkin da shugaban Assisi ya jagoranta wanda ya kifar da gwamnatin Muhammad Mursi a cikin watan yulin shekara ta 2013 ne gwamnatin kasar Masar take dirar mikiya kan masu adawa da gwamnatin kasar. 

Tags