Aug 29, 2018 06:39 UTC
  • An Cabke Wasu Jami'an Tsaro Kan Laifin Cin Zarafin'Yan Majalisa A Uganda

An cabke wasu jami'an tsaron kasar Uganda da suka ci mutuncin 'yan majalusun kasar bisa zargin su nada hanu da jifan tawagar shugaban kasa.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa a ranar 13 ga wannan wata na Augusta mabiya bayan wani dan takara mai zaman kansa sun yi ruwan duwatsu ga tawagar shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni  yayin da yake yakin neman zabe a garin Arua.

Bayan aukuwar lamarin, jami'an tsaro sun cabke wasu mutane ciki har da wasu 'yan majalisun kasar, inda suka ci mutuncinsu, kama daga zagi harda ma duka.

Wannan lamari dai ya janyo zanga-zangar kin jinin gwamnati na kwanaki biyu a Kampala babban birnin kasar.

A ranar Litinin din da ta gabata, shugaban Majalisar dokokin kasar ta Uganda Mista Rebecca Kadaga ya rubutawa shugaban kasar wasika, inda ya bukaci a kame wadannan jami'an tsaro sannan kuma a gurfanar da su a gaban  Kotu.

Tags