Aug 30, 2018 06:23 UTC
  • An Halaka Yan Ta'adda 20 A Yankin Sinaa Na Kasar Masar

Majiyar jami'an tsaro a kasar Masar ta bayyaba cewa a cikin yan kwanakin da suka gabata sun halaka yan ta'adda a kalla 20 a yankin Sinaa.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya nakalo wani babban jami'in soja a kasar ta Masar yana fadar haka a jiya Laraba ya kuma kara da cewa Jami'an tsaron kasar sun sami nasarar rusa mabuyar yan ta'adda har guda 18 da kuma gano rumbunan makamai a wuraren. Banda haka sun kwance boma boman wadanda aka dasa su a kan tituna a yankin har guda 41. 

Labarin ya kara da cewa jami'an tsaron sun kama yan ta'adda 81 da ransu a yayinsa suka kwace motoci 39 dauke da makamai masu yawa. 

Tun cikin watan Jenerun shekarar da muke ciki ne jami'an tsaron kasar Masar suka fara wani shiri na musamman da nufin kawo karshen yan ta'adda musamman na kungiyar "Walayatu Sinaa" a yankin. 

Tags