Sep 01, 2018 06:33 UTC
  • An Kama Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Uganda A Lokacinda Yake Kokarin Fita Daga Kasar

Jami'an tsaro a kasar Uganda sun kama wani dan majalisar dokokin kasar dan wata jam'iyyar adawa a dai dai lokacinda yake kokarin tafiya kasashen waje don jinyar raunin da aka ji masa a kamu na baya.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya ce Jami'an tsaron Uganda sun kama Robert Kyagulanyi a tashar jiragen sama na Entebbe sannan aka tafi da zuwa birnin Kampala aka kwantar da shi a wani asbiti.

Kafin haka dai Kyagulanyi yana tsananin sukar gwamnatin Yuwere Musenene a majalisar dokokin kasar, sannan an sha kama shi sanadiyyar sukar gwamnatin kasar. Sai kuma a ranar litinin da ta gabata ce aka bada belinsa a tsare shi na karshe da aka yi, sai kuma a ranar Alhamis aka hana shi fita daga kasar don jinya. 

An zargin Robert Kyagulanyi da wasu mutane 32 da laifin kokarin yin jifa kan motar shugaban kasa a yankin Arua a ranar 14 ga watan Augustan da muke ciki a lokacin da shugaban ya je yankin don yakin neman zabe wa yan jam'iyyarsa a zaben majalisar dokokin da za'a gudanar nan gaba.

Tags