Sep 03, 2018 19:02 UTC
  • Najeriya: An Sami Karuwar Sojojin Da Boko Haram Su Ka Kashe

Majiyar sojan Najeriya ce ta sanar da karuwar wadanda su ka kwanta dama sanadiyyar harin na 'yan ta'addar Boko Haram akan iyaka da kasar Nijar.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ambato majiyar sojan kasar ta Najeriya tana cewa Adadin sojojin da su ka kwanta dama sun kai 48. Da fari majiyar sojan na Najeriya ta sanar da kashe sojoji 30 a harin na ta'addanci.

Majiyar ta kara da cewa; Baya ga wadanda su ka kwanta dama an sami wasu sojojin masu yawa da su ka jikkata.

Wannan harin yana daga cikin hare-hare mafi muni da sojojin Najeriya su ka fuskanta daga kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram.

A ranar 18 ga watan Agusta na 2018 kungiyar ta boko haram ta kai wasu hare-hare masu mini a kauyukan da suke jahar Borno.

Tun a 2009 ne dai kungiyar ta fara kai hare-hare a cikin Najeriya wanda kawo ya zuwa yanzu ta kashe fiye da mutane 20,000 da kuma tialsta wa mutane miliyan 2 da 600,000 yin hijira.

Tags