Sep 06, 2018 16:42 UTC
  • Sojojin Nijeriya Sun Ce Sun Hallaka 'Yan Boko Haram Da Dama

Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa dakarunta sun sami nasarar hallaka wani adadi mai yawa na 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Daraktan bangaren hulda da jama'a na rundunar, Birgediya Janar Texas Chukwu, ne ya shaida hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis inda ya ce dakarun na su da suke aiki karkashin dakarun  Operation Lafiya Dole ne suka sami wannan nasarar bisa daukin da suka samu daga wajen dakarun bataliya ta 82 na rundunar sojin da aka tura su jihar ta Borno.

Janar Chukwu ya ce dakarun sun kai harin ne bayan wani bayani da suka samu dangane da 'yan Boko Haram din a kauyen Gesada, inda suka sami nasarar hallaka 'yan Boko Haram din da dama wadanda suka zo kauyen da nufin satan kudade da kuma yin gaba da dabbobin mutanen kauyen.

Daraktan ya ce daga cikin kayayyakin da aka kwace a wajen 'yan ta'addan har da bindigogi samfurin AK 47 bugu da kari kan wasu dabbobi da 'yan ta'addan suka kwace daga wajen masu shi.

 

Tags