Sep 07, 2018 19:05 UTC

A yau ne jagoran Harkar Muslunci a Najeriya ya cika kwanaki 1000 a tsare a hannun jam'ain hukumar tsaro ta kasa DSS.

Mabiya Harkar Muslunci a Najeiya (Islamic Movement in Nigeria) sun sake jaddada kira ga gwamnatin  Najeriya da ta saki jagoran Harkar Muslunci Sheikh Ibrahim Zakzaky, wanda ake tsare da shi yau kwanaki 1000 duk kuwa da umarnin da kotun tarayya ta bayar na a sake shi.

A kan wannan batu mun tuntubi shugaban dandalin watsa labarai na Harkar Musulunci Malam Ibrahim Musa, ya kuma yi mana karin bayani kamar yadda za a ji:

Tags